Kannywood: Ali Nuhu da matarsa sun cika shekara 16 da aure

Kannywood: Ali Nuhu da matarsa sun cika shekara 16 da aure

Fitaccen jarumin nan na Kannywood wanda ake yiwa lakabi da Sarki mai Kannywood mai sangaya, Ali Nuhu da Uwargidarsa Maimunatu sun cika shekaru 16 da aure.

Jarumin ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook inda ya nemi a taya su da addu’a da kuma fatan alkhairi kan Allah ya cci gaba da kara dankon soyayya a tsakaninsu.

Ma’auratan dai sun yi aure ne a watan Maris na shekarar 2003, sannan kuma Allah ya albarkace su da haihuwar yara biyu, mace daya, namiji daya wato Fatima da Ahmed.

Ga yadda jarumin ya rubuta a shafinsa na Facebook: “Alhamdulillah, yau mun cika shekaru 16. Muna godiya ga Allah SWT da ya nuna mana wannan ranar, sannan ya kara dankon soyayya tsakanin mu. Yan’uwa da abokan arziki a taya mu da addua.”

Wannan abun alfahari ne ga ma’auratan duba ga yadda ake fuskantar yawan mace-macen aure a tsakanin jaruman fim dama yankin Arewa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel