Rikicin jihar Taraba ya kara zafi, an kara tsaurara doka hana jama’a fita

Rikicin jihar Taraba ya kara zafi, an kara tsaurara doka hana jama’a fita

A yayin da rikici a garin Jalingo ke kara tsamari, gwamnatin jihar Taraba ta kara tsawon lokacin hana jama’a fita daga gidajen a babban birnin jihar, Jalingo.

A jiya ne gwamnatin jihar Taraba ta saka dokar hana jama’a fita daga gidajen su daga karfe 6:00 na yamma, sai ga shi yanzu ta mayar da dokar zuwa sa’a 24.

A sanarwar da Bala Dan Abu, babban mai taimakawa gwamnan jihar Taraba a bangaren yada labarai, ya fitar ya ce gwamnatin jihar ta kara tsaurara dokar ne domin tabbatar da zaman lafiya tare da bayyana cewar sabuwar dokar za ta cigaba da aiki har zuwa lokacin da za a samu sabuwar sanarwa daga gwamnati.

Yawaitar kai hare-hare a kan mazauna wasu sassan garin Jalingo tun ranar Juma’a ne ya sa gwamnatin jihar ta fara saka dokar hana fita a ranar Lahadi.

Rikicin jihar Taraba ya kara zafi, an kara tsaurara doka hana jama’a fita
Rikicin jihar Taraba ya kara zafi, an kara tsaurara doka hana jama’a fita
Asali: Facebook

Amma bayan al’amura sun kara zafafa a garin a jiya Litinin, gwamnatin jihar ta yanke shawarar kara tsaurara dokar a yau.

DUBA WANNAN: Na yaga sakamakon zabe ne domin kare dimokradiyya – wakilin dan takarar gwamna a PDP

Wata majiya ta shaida mana cewar jama’a da dama sun kauracewa gidajensu tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a garin.

An tura Karin jami’an soji domin cigaba da sintiri a titunan garin yayin da jirgin rundunar soji ke shawagi a sararin samaniyar garin.

Ya zuwa yanzu babu kididdigar asarar dukiya ko ta rayuka sakamakon hare-haren da aka kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel