Zaben Gwamna: Jam'iyyar APC ta yi nasara a jihar Yobe
Da sanadin shafin jaridar The Cable mun samu cewa, dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya lashe zaben gwamnan jihar Yobe kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta zayyana.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Mala Buni, ya lashe zaben jihar Yobe da kimanin kuri'u 444,013, inda ya lallasa abokin adawar sa na jam'iyyar adawa ta PDP, Umar Bello Iliya, da ya samu gamayyar kuri'u 95,703.

Asali: Original
KARANTA KUMA: Majalisar Jiha: APC ta lashe Kujeru 12, PDP ta samu 3 a jihar Kano
A jiya Lahadi jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, shine ke kan gaba yayin da ya lashe sakamakon zaben kananan hukumomi 9 na jihar Yobe.
Ga yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Yobe ya kasance cikin wasu kananan hukumomi 9 kamar yadda hukumar INEC ta tabbatar.
Karamar Hukumar Damaturu
APC: 26,087
PDP: 3,760
Karamar Hukumar Bade
APC: 32,213
PDP: 8,854
Karamar Hukumar Karasuwa
APC: 24,263
PDP: 2,762
Karamar Hukumar Bursari
APC: 20,657
PDP: 2,813
Karamar Hukumar Gulani
APC: 21,765
PDP: 4,576
Karamar Hukumar Fika
APC: 36,519
PDP: 9,552
Karamar Hukumar Tarmuwa
APC: 11,338
PDP: 3,925
Karamar Hukumar Nangere
APC: 25,698
PDP: 4,765
Karamar Hukumar Gujba
APC: 17,714
PDP: 1,119
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng