Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari

Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin cewa zai kara zage damtsen aiki sosai a wannan karon

- Buhari ya sha alwashin magance kalubalen da kasar ke fuskanta

- Zababben shugaban kasar yace ba zai ba yan Najeriya kunya ba a wannan zangon nasa na karshe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya tabbacin cewa zai kara zage damtsen aiki sosai a wannan karon domin magance kalubalen da kasar ke fuskanta.

Da yake Magana da shugabanin kungiyar Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) da suka kai masa ziyarar taya murna a Villa, Abuja, Shugaban kasar ya bayyana cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba.

Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari
Zan zage damtsen aiki sosai a wannan karon - Buhari
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Shugaban kasa Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa wanda ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Buhari ya samu kuri’u 15,191,847 inda ya kayar da abokin adawarsa, Atiku wanda samu kuri’u 11,262,978.

Shugaban kasar ya kuma yi godiya ga mambobin kungiyar ACF kan ziyarar da suka kai masa inda yace: “Wannan shine zangona na karse. Zan yi kokari domin ganin nayi aiki sosai. Ina baku tabbacin cwa b azan baku kunya ba.

KU KARANTA KUMA: Yan takarar gwamna 9 sun janye daga tseren a Adamawa

Shugaban kungiyar amintattu na ACF, Alhaji Adamu Fika, wanda ya jagoranci tawagar yace sun kai ziyarar ne domin taya Shugaban kasar murnar nasarar da yayi a zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel