Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari

Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari

Labarin mutuwar Bala Haruna, dan asalin jihar Bauchi wanda ya kasance babban masoyin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi fice a ranar Talata, 5 ga watan Maris.

Haruna ya sha alwashin kwashe mintuna 10 a cikin kwata sannan ya sha ruwan kwatan idan har shugaba Buhari ya lashe zaben Shugaban kasa.

A take ranar da aka kaddamar da Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu, Haruna ya cika alkawarin da ya dauka kamar yadda ya shiga kwatan sannan ya sha ruwan dattin da ke ciki.

Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari
Dan asalin jihar Bauchi ya mutu yan kwanaki kadan bayan yayi wanka da shan ruwan kwata don murnar nasarar Buhari
Asali: Twitter

Hakan ya sa shi yin fice kafafen watsa labarai bayan hotonsa ya shahara a yanar gizo.

Sai dai kuma a ranar Talata, 5 ga watan Maris labarin mutuwarsa ya fito bayan yayi fama da matsalar fashewar hanji a asibiti yan kwanaki bayan shaharan da yayi.

KU KARANTA KUMA: EFCC na kokarin karbe hujjojin Atiku na zuwa Kotu - CUPP

A cewar jaridar The Guardian, an yi gaggawan kai Haruna asibiti bayan yayi korafin ciwon ciki mai tsanani da kuma kashin jini na tsawon kwanaki biyu.

Bayan yan gwaje-gwaje da aka gudanar, an gano cewa ya kamu da kfashear hanji wanda ya kamu dashi ne ta ruwan kwatan da ya sha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel