Ka daina sukar Buhari, ka nema wa kanka hutu a shekara 82 - Alake ya shawarci Obasanjo

Ka daina sukar Buhari, ka nema wa kanka hutu a shekara 82 - Alake ya shawarci Obasanjo

Alake kuma sarki a kasar Yarbawa, Oba Aremu Gbadebo, a ranar Talata ya shawarci tsohon shgaban kasa Olusegun Obasanjo da ya rabu da sukar da yake yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Basaraken ya bada shawarar ne a sakon taya Obasanjo murnar zagayowar ranar haihuwarsa na shekara 82 a dakin karatunsa da ke Abeokuta.

Gbadebo, wanda ya bayyana cewa Obasanjo ya kasance gwarzo a rayuwarsa gaba daya, ya bukace shi da ya huta.

Da farko, tsohon ministan harkokin gida a Afurka ta kudu, Mista Mangosuthu Buthelezi, ya gabatar da lacca mai take: “Colnialism Apartheid, Freedom and South Africa Rising.’’

Ka daina sukar Buhari, ka nema wa kanka hutu a shekara 82 - Alake ya shawarci Obasanjo
Ka daina sukar Buhari, ka nema wa kanka hutu a shekara 82 - Alake ya shawarci Obasanjo
Asali: UGC

Buthelezi, a laccan, ya bayyana cin hanci a matsayin babban kalubale da yankin Afirka ke fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Mambobin jam’iyyar PDP, ADP, DPN sun sauya sheka zuwa APC a Lagas

Ya bayyana damuwarsa cewa a halin yanzu Afirka ta kudu ta kasance tsundume a cikin rashawa a tsarin matakai na Corruption Perceptions Index of the Transparency International.

Tsohon ministan Afirka ta kudun ya danganta lamarin ga “kurakurai da aka tafka, hadama da keta akan albarkatun kasa”.

Buthelzi, wanda ya bayyana cewa kashi shida a cikin kungiyan kasashen Afirka sun hau mataki na 50 a manuniya, ya karfafa cewa rashawa ta karkatar da yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel