Atiku ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya

Atiku ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 82 a duniya

- A yau Talata, 5 ga watan Maris ne tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya cika shekaru 82 duniya

- Atiku Abubakar ya taya shi murna tare da fatan alkhairi

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya cika shekaru 82 duniya a yau Talata, 5 ga watan Maris. Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya taya shi murna a safiyar yau.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon mataimakin Shugaban kasa yace: “Ina taya ka murnar shika shekaru 82, Cif Olusegun Obasanjo. Babu wani dan Najeriya a raye da ya ba kasar nan zaman lafiya a lokacin yaki kamar kai.

“Allah Ubangiji ya karo maka shekaru masu yawa cikin koshin lafiya sannan ka ci gaba da yiwa Najeriya da duniya baki daya aiki."

KU KARANTA KUMA: Wani matashi ya kashe makwabciyarsa saboda ta tambaye shi ranar da zai yi aure

A wani lamari na daban, mun ji cewa hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta saki surukin Atiku, Babalele Abdullahi, kuma akawun manyan kamfanonin da Alhaji Atiku Abubakar ya mallaka.

An damke surukin Atikun ne ranan Asabar amma aka sake shi bayan ta gayyaci lauyansa, Tanimu Turaki, wanda aka damke ranan Litinin. Kakakin EFCC, Tony Orilade, ya tabbatarwa The Cable cewa an damkesa amma bai bada cikakkun bayanai.

Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyanawa manema labarai cewa Tanimu Turaki ne babban lauyan da ke shirin kai karan shugaba Buhari kotu kan zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel