Kalli yadda Aisha Buhari ta taka rawa bayan mijinta ya lashe zabe (bidiyo)

Kalli yadda Aisha Buhari ta taka rawa bayan mijinta ya lashe zabe (bidiyo)

Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha ta yi yar karamar liyafa domin taya mai gidanta nasarar da yayi na sake lashe zaben shugabancin Najeriya a karo na biyu.

An gano Aisha Buhari tare da ahlinta da wasu manyan mata inda suke chashewa suna rawa cikin farin ciki da annashuwa.A safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu ne dai Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya kaddamar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa da ya gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Kalli bidiyon wanda aka wallafa a shafin Instagram:

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matasan Arewa sun jero kura-kurai 6 a gudanarwar zaben Shugaban kasa na 2019

A safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu ne dai Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya kaddamar da shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa da ya gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na cikin wata ganawa domin sake duba zaben Shugaban kasa da na yan majalisa da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata. Ganawar wanda ke zuwa yan sa’o’i bayan zaben na gudana ne tsakanin tawagar hukumar INEC da kwamishinonin zabe.

A jawabin bude taro, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a sake duba ga tsarin da kuma matakan da aka bi sannan ayi gyara inda bukatar hakan ta taso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel