Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa

Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa

- Tawagar hukumar zabe mai zaman kanta da kwamishinonin zabe na cikin ganawar sirri a yanzu haka

- Hukumar INEC na gudanar da ganawar ne don sake duba zaben Shugaban kasa da na yan majalisa da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata

- Shugaban INEC, Farfesa Mahmood yace ganawar zai taimaka wajen kammala tsare-tsare na zaben gwamnoni da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na cikin wata ganawa domin sake duba zaben Shugaban kasa da na yan majalisa da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Ganawar wanda ke zuwa yan sa’o’i bayan zaben na gudana ne tsakanin tawagar hukumar INEC da kwamishinonin zabe.

Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa
Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa
Asali: UGC

A jawabin bude taro, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a sake duba ga tsarin da kuma matakan da aka bi sannan ayi gyara inda bukatar hakan ta taso.

Ya kuma bayyana cewa ganawar zai taimaka wajen kammala tsare-tsare na zaben gwamnoni da ke zuwa a jihohi 29 na tarayyar kasar da kuma zaben kwamiti na birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya ya cika alkawarin da ya dauka na shiga kwata idan Buhari yayi nasara (hoto)

A baya mun ji cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kujeru mafi rinjaye a sabuwar majalisar dattawan da za'a shiga inda ta samu kujeru akalla 64 a zaben da ya gudana ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Jam'iyyar adawa da Peoples Democratic Party (PDP) ta samu kujeru 40, jam'iyyar YPP ta samu kujera daya kacal, yayinda sauraron sakamakon kujeru 2 daga jihar Plateau, 1 daga jihar Taraba, da daya daga jihar Imo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel