APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba

APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe kujerar sanata a yankin kudancin Bauchi.

Jam’iyyar ta samu kuri’u 250,725 yayinda dan takarar jam’iyyar PDP, Garba Dahiru ya samu kuri’u 175,527.

Sai dai kuma INEC ba t bayyana Sanata Lawal Yahaya Gumau a matsayin dan takarar APC ba a zaben kamar yadda jami’in zaben, Farfesa Sarki Ahmed Fagam bai ambaci sunansa ba yayin sanar da sakamakon zaben; lamarin da ya tayar da wasu alamomi na tambaya.

Da yake bayani akan dalilin bayan sanar da sakamakon, kwamishinan zabe na jihar, Ibrahim Abdullahi, yace APC ce ta lashe zaben amma kuma babu dan takara.

APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba
APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba
Asali: Facebook

A cewarsa Shugabannin APC ba su ba umurnin kotu hadin kai ba wanda ya umurce su da maye gurbin Gumau da wani bayan an cire shi.

KU KARANTA KUMA: Ina son zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya – Gudaji Kazaure

Kwamishinan zaben ya jadadda cewa APC ce tayi takara a zabeen tunda bata gabatar da wani dan takara ba kamar yadda aka yi umurni.

Da aka kira sakataren gudanarwa na APC a jihar Bauchi, Lawan Gyan-Gyan, yaki cewa komai akan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel