Manyan jiragen dankaro guda 13 sun shigo Najeriya dauke da man fetir

Manyan jiragen dankaro guda 13 sun shigo Najeriya dauke da man fetir

A yanzu haka wasu manya manyan jiragen dankaro na cikin ruwa guda goma sha uku sun fara sauke kayan da suka dauko daga sassan duniya suka shigo dasu Najeriya a tashoshin jiragen ruwan Najeriya dake jahar Legas.

Legit.ng ta ruwaito hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA ce ya bayyana haka cikin sanarwar da take fitarwa a kullu yaumin, inda tace jiragen goma sha uku suna sauke kayan nasu ne a tashar Apapa da tashar tsibirin Tincan.

KU KARANTA: Mummunan kisa: Uwargida ta tuntsuro Maigidanta daga gidan sama a jahar Kano

Hukumar NPA ta bayyana cewa daga cikin jiragen akwai guda daya dake dauke da man dizil, kuma ya fara sauke man ne da sanyin safiyar Laraba, 27 ga watan Feburairu, kamar yadda hukumar ta tabbatar.

Sauran abubuwan da jiragen sauran jirage goma sha biyu suka dauko sun hada da man fetir, pulawa, sundukai, siga, man jiragen sama, da kuma sauran hajojin yan kasuwan Najeriya daban daban da suka yo odansu.

A wani labarin kuma, al’ummar kasar Najeriya na cikin halin farin ciki tun bayan da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasar daya gudana a karshen makon daya gabata, watau shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A daren Laraba 27 ga watan Feburairu ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel