Jam’iyyar PDP tayi nasara a akwatin gidan Namadi Sambo

Jam’iyyar PDP tayi nasara a akwatin gidan Namadi Sambo

Mun samu labari cewa ‘dan takarar babban jam’iyyar adawa na PDP watau Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a akwatin da tsohon mataimakin shugaban kasa Arch. Namadi Sambo ya saba zabe.

Jam’iyyar PDP tayi nasara a akwatin gidan Namadi Sambo
Buhari ya rasa akwatin Namadi Sambo a Kaduna
Asali: Depositphotos

Alhaji Atiku Abubakar ya rasa akwatin zaben Mohammed Namadi Sambo a Garin Kaduna inda yake kada kuri’ar sa. Jam’iyyar PDP ta samu kuria’ 207 ne a zaben shugaban kasa yayin da APC mai mulki kuma ta samu kuri’a 34 rak.

A yau ne aka sanar da sakamakon zaben yankin inda aka tabbatar da cewa PDP ce ta lashe rumfar. Hajara Lawal ita ce jami’ar zaben da ta sanar da wannan sakamako kamar yadda mu ka samu labari daga ‘yan jaridan kasar.

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan Kaduna El-Rufai ya sha kasa a cikin Garin sa

A zaben ‘yan majalisun tarayya kuma, jam'iyyar APC ta samu kuri’a 30 rak ne a kujerar ‘dan majalisa, inda PDP kuma ta samu kuri’a 117. Sanatan Yankin mai-ci Kwamared Shehu Sani na jam’iyyar PRP kuma ya samu kuri’a 92 a zaben.

Hajiya Hajara Lawal ta kuma sanar da cewa jam’iyyar APC mai mulki ta samu kuri’a 30 a zaben wakilan tarayya. ‘Dan takarar PRP ya samu kuri’a 19 a zaben inda PDP mai adawa a jihar ta samu nasara da kuri’a 194 inji Malamar zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel