Babu wanda ya isa ya kawo mani kudi domin ayi murdiya – Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano

Babu wanda ya isa ya kawo mani kudi domin ayi murdiya – Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano

Mun samu labari cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano watau CP Muhammad Wakili ya bayyana cewa ba ya bari a hada kai da shi domin ayi duk wani aikin Ma-sha-Ah a inda yake aiki.

Babu wanda ya isa ya kawo mani kudi domin ayi murdiya – Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano
CP na Kano yace bai bada fuskar karbar yin aikin assha ba
Asali: UGC

Sabon kwamishinan ‘yan sandan na jihar Kano yayi hira a gidan rediyo kwanan nan inda yake cewa babu wanda yake tsoro a Duniya sai Ubangijin da ya halicce sa. CP M. Wakili yake cewa shi mutum ne mai riko da gaskiya.

Kwamishinan ‘Yan Sandan ya nuna cewa yana tsoron haduwa da Mala’ikan kabari idan ya mutu yana mai laifi. Babban jami’in ‘yan sandan yake cewa babu wanda yake neman sa da nufin yayi abin da bai dace ba a bakin aikin sa.

KU KARANTA: Atiku da PDP sun yi nasara a akwatin zaben Kwankwaso a Madobi

Sabon kwamishinan da aka aiko jihar Kano daf da zaben bana yake cewa ko da an nemi a hada baki da shi domin ayi rashin gaskiya, ba zai bari ba. Ya kuma bayyana cewa ba ya bada fuskar da har za a tunkare sa da batun assha.

Muhammad Wakili yake cewa bai bada damar da wasu bata-gari za su neme sa da yayi abin da ya sabawa aikin sa ba. Jami’in tsaron ya dai bayyana cewa bai taba zuwa ofishin gwamna Abdullahi Ganduje tun da aka turo sa jihar Kano aiki ba.

Dazu kun ji cewa Ƴan Sanda sun azabtar da Ma’aikatan zaɓe a Garin Kura a Kano. Jami’an tsaron sun barbadawa Turawan da ke neman aikin zabe hayaki ne bayan rikici ya nemi ya barke a ofishin INEC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel