Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure

Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure

A yau Juma'a 22 ga watan Fabrairu ne manhajar sauya kudade ta Google Currency ta bayyana cewar darajar dallan Amurka guda dai-dai ya ke da N184 a kudin Najeriya amma daga baya an gano cewa kuskure ce ne aka samu.

The Cable ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN ta sayar da dallan Amurka guda a kan N357 a yau Juma'a.

Wani dan canji, Musa Ibrahim da ya yi hira da majiyar Legit.ng daga Legas ya ce ya saya $20,000 daga CBN a kan N357 ko wace dala.

Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure
Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zabe: Jiha daya a kudu, biyu a arewa sun kere ragowar a yawan ma su kada kuri'a

Mun saya dalla daga CBN a kan N357, kuma ko wane mai sana'ar canji yana da damar sayan dallar $20,000.

A cewar manhajar canjin kudi ta Bloomberg, a halin yanzu ana sayar da dallan Amurka ne a kan N361.8 wadda hakan na nuna cewa naira ta kara daraja a kan dallar Amurka da N1.75.

A halin yanzu dai ofishin Google ba ta amsar sakon e-mail da aka aike mata ba ne neman karin bayani a kan farashin naira da dalla da manhajar ta na canjin kudi ya ke nunawa.

Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure
Farashin dala: Ku kwantar da hankulan ku, Google ne ya yi kuskure
Asali: UGC

Wannan sabuwar farashin na dala da manhajar Google ke nunawa ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta inda wasu ke ba'ar cewa gwamnati ne tayi inganta darajar naira cikin dare guda saboda al'umma su zabe ta.

Wasu kuma hakan ya sanya sun razana saboda ganin suna da dololi da idan har hakan ta faru kudin su zai karye sosai sai dai a yanzu mutane da yawa sun gano cewa matsala ce aka samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel