Ku fita ku yi zabe – Buhari ga yan Najeriya

Ku fita ku yi zabe – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci masu zabe kan bukatar su fita su cika hakkin da ya rataya a wuyansu a matsayinsu nay an kasa ta hanyar fita su zabi dan takarar da suke so a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasa a jawabi da yayi wa kasa baki daya a ranar Juma’a a Auja yace haakki ne duk wanda ya isa zabe ya fita ya zabi gwamnatin da za ta jagoranci Najeriya zuwa inda take mafarkin zuwa.

Ya bayyana cewa akwai bukatar yin kiran ne domin zabe shine mafi girman yanci day an kasa ke da shi ta yadda za su yi zabin gwamnatin da suke so ya wakilce su da kansu.

Ku fita ku yi zabe – Buhari ga yan Najeriya

Ku fita ku yi zabe – Buhari ga yan Najeriya
Source: UGC

A cewar Shugaban kasar, ta hakan ne mutanen za su samu muradin ransu wato gwamnati da za ta jajirce wajen tabbatar da jin dadin mutane da kuma kare hakkinsu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi jan kunne ga Buhari da Ganduje idan har wani abu ya samu Kwankwaso

Shugaban kasar ya kuma yi kira ga al’umman kasar da kada su bari wani ya karya masu gwiwa ta hanyar hana su fita su yi zabe a ranar Asabar.

Ya kuma ce kada su bari a tsorata su da rade-radin cewa rikici zai kaure a yayin zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel