Babbar kotun Najeriya ta bada umarnin a cafko mata babban dan kwallon Najeriya

Babbar kotun Najeriya ta bada umarnin a cafko mata babban dan kwallon Najeriya

Wata babbar kotun jahar Legas ta bada umarnin a cafko mata babban dan kwallon Najeriya, Austin Okocha wanda aka fi sani da suna Jay Jay Okocha, a duk inda yake, sakamakon kararsa da aka shigar a gabanta, kuma yaki gurfana a gabanta.

Gwamnatin jahar Legas ce ta shigar da karar Okocha gaban kotun akan tuhumarsa da take yin a kin biyan harajin kudaden shiga daya samu, kamar yadda lauyan gwamnati, Jide Martins ya shigar da karar a ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2017.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kano ta garkame ofishin Sheikh Daurawa na sakatariyar Hisbah

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tun a ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2017 aka fara sauraron karar, amma har yanzu Okocha bait aba gurfana gaban kotun ba, duk kuwa da umarnin da Alkalin kotun, Mai sharia Adedayo Akintoye ya bayar na ya gurfana a gaban kotun.

Lauyan gwamnati Jide ya shaida ma kotu cewa dan kwallon baya son biyan haraji ga gwamnati, inda yace hakan ya saba ma sashi na 56 (a) da (b) na kundin dokokin haraji na jahar Legas, da kuma sashi na 94 (1) na dokokin Najeriya.

A wani labarin kuma, wasu gungun Mata sun yi namijin kokari wajen tseratar da wata tsohuwa da wasu barayin mutane suka yi kokarin yin garkuwa da ita a garin Jalingo na jahar Taraba, bayan sun yi arangama dasu a tsakiyar titi.

Da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Alhamis ne wasu gungun barayin mutane su biyar suka kama wata mata mai suna Malama Haruna suka jefata a cikin Keke Napep din da suke ciki, inda suka yi kokarin tserewa da ita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel