Wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ya shiga hannun hukuma a Katsina

Wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ya shiga hannun hukuma a Katsina

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wani kasurgumi kuma gagararren mai garkuwa da mutane da ta dade tana farautarsa a jahar Katsina, kamar yadda rundunar ta bayyana a ranar Laraba, 20 ga watan Feburairu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansanda dake cikin garin Katsina, inda ya bayyana yadda suka samu nasarar cafke wannan mugun mutum.

KU KARANTA: Da dumi dumi: JAMB ta daga ranar zana jarabawar shiga jami’a

Kaakaki Gambo yace jami’an Yansanda sun yi nasarar kama barawon mai suna Magaji Gudaji ne bayan kimanin kwanaki biyar da yayi barazanar yin garkuwa da wani fitaccen attajiri a garin Malumfashi idan har bai bashi kudi naira miliyan biyu ba.

Kaakakin ya bayyana shekarun Magaji a Talatin daidai, kuma mazaunin kauyen Yandoka ne ake cikin garin Dayi ta karamar hukumar Malumfashi, inda yace sai bayan kwanaki biyar da yin barazanar ne suka samu nasarar kamashi bayan wani ya tsegumta musu inda yake.

Bayan sun kamashi, Yansanda sun kama wata wayar hannu samfurin Itel da layin waya daga hannunsa, haka zalika sun kamashi da wata wasikar barazana daya rubuta da hannunsa zai kai ma attajirin garin Malumfashin.

Duk da cewa wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa kamar yadda kaakakin Yansandan jahar ya bayyana, amma yace zasu cigaba da gudanar da bincike domin samun karin bayani daga gareshi ta yadda zasu kama sauran abokan aikinsa.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan jahar Nassarawa ta tabbatar da sace wani basaraken gargajiya, dakacin kauyen Gida-Bakin Kogi dake cikin karamar hukumar Lafiya ta jahar Nassarawa, Alhaji Yakubu Dauda da ake zargin wasu yan bindiga sun aikata.

Rundunar Yansandan ta tabbatar da haka ne a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu ta bakin kaakakinta, Samaila Usman, wanda ya bayyana cewa da misalin karfe 1:25 na daren Litinin yan bindigan suka yi awon gaba da Yakubu daga gidansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel