Mai kwadayi shi ya san gidan mai rowa: Ghana ta fatattako yan Najeriya 723

Mai kwadayi shi ya san gidan mai rowa: Ghana ta fatattako yan Najeriya 723

Jakadan Najeriya a kasar Ghana, Michael Abikoye ya bayyana bacin ransa da matakin da kasar Ghana ta dauka na wartako yan Najeriya dake zaune a kasar da adadinsu ya kai dari bakwai da ashirin da uku, 723, daga shekarar 2018 zuwa 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jakada Abikoye ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasar Ghana, GIS, Kwame Takyi a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Kai jama’a: Yan bindigan sun sace dakacin kauye sukutum a jahar Nassarawa

A jawabin Abikoye, yace hukumar GIS ta fake da cewa yan Najeriya na aikata laifukan da suka danganci karuwanci, satar yanar gizo, da kuma ba bisa ka’ida, Daga cikin wadanda aka wartako akwai 81 da aka kama da laifin satar yanar gizo, yayin da 115 kuma keda laifin karuwanci da zama ba bisa ka’ida ba.

Sai dai Abikoye ya bayyana bacin ransa da yadda ka ci zarafin yan Najeriyan da jami’an kasar Ghana suka wartako, inda yace Najeriya ba zata lamunci irin wannan cin mutuncin ba, amma ya tabbatar da cewa ita kanta Najeriya ba wai tana goyon bayan masu aikata laifi bane, tana jan kunne ne akan ketar da ake nuna ma yan Najeriya a Ghana.

“Ai bai kamata ace an wartaki yan Najeriya mazauna Ghana akan zama ba bisa ka’ida ba, akwai yan Ghana da dama dake zaune a Najeriya, kuma hukumar kula da shige da fice ta Najeriya bata taba korarsu akan laifin zama ba bisa ka’ida ba saboda amintakar dake tsakaninmu dasu.

“Mun samu rahoton cin zarafin yan Najeriya, musamman wadanda aka kama da nufin dawo dasu Najeriya, ana cin zalinsu, ana cin mutuncinsu tare da cutar dasu a wuraren da ake ajiye dasu.” Inji shi.

Daga nan Jakadan ya mika ma shugaban hukumar GIS hotunan wasu daga cikin yan Najeriyan da suka fuskanci irin wannan cin zarafin, wasu da karyayyun kafafuwa da hannaye, wasu kuma sun samu rauni a ido a sanadiyyar haka.

Sai dai a jawabinsa, shugaban GIS ya tabbatar da amintakar dake tsakanin Najeriya da Ghana, sa’annan ya bayyana cewa dole ce tasa suke wartako yan Najeriya sakamakon miyagun halayyar da wasunsu suke nunawa a Ghana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel