Mataimakin Kakakin Majalisar Yobe, Dr. Ibrahim Kurmi ya rasu jiya

Mataimakin Kakakin Majalisar Yobe, Dr. Ibrahim Kurmi ya rasu jiya

- An yi rashin Mataimakin Kakakin Majalisr Dokokin na Jihar Yobe

- Garba Ibrahim Kurmi mai wakiltar YankinFika ya rasu ne a jiya

- ‘Dan Majalisar yayi fama da ‘yar rashin rashin lafiya kafin ya cika

Mataimakin Kakakin Majalisar Yobe, Dr. Ibrahim Kurmi ya rasu jiya

Yau Talata za yi jana’izar Honarabul Garba Ibrahim Kurmi
Source: Facebook

Mun samu labari cewa daya daga cikin manyan majalisar jihar Yobe ya rasu kwanan nan. Dr. Garba Ibrahim Kurmi wanda kafin cikawar sa shi ne mataimakin majalisar dokokin jihar ta Yobe ya bar Duniya ne a jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari ba da dadewa ba, Honarabul Garba Ibrahim Kurmi mai wakiltar yankin Fika da Ngalda a majalisar jihar Yobe ya rasu ne a asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Yobe da ke cikin Garin Damaturu.

KU KARANTA: Wasu 'yan iska sun sace wani Jigon PDP a Jihar Adamawa

'Dan majalisar na yankin Fika I da ke shiyyar kudancin jihar Yobe ya fara wakiltar mazabar sa ne tun a shekarar 2011. Hon. Garba Ibrahim Kurmi ya rasu ne bayan ‘yar takaitacciyar rashin lafiya da yayi ta fama da ita inji Iyalin sa.

Bayan kasancewar sa mataimakin kakakin majalisa, Marigayin shi ne kuma shugaban kwamitin tsaro da kuma korafe-korafe a majalisar. Haka kuma yana cikin jagororin da ake da su na wasu kwamitoci da dama a majalisa.

Desert Herald tace yau Talata za yi jana’izar wannan Bawan Allah kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Marigayin ya rasa tikitin tazarce a APC bana bayan ya sha kashi a zaben tsaida gwani a hannun Yakubu Suleiman Malori.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel