Dakatar da Alkalin Alkalai na Najeriya ya sabawa doka ta Duniya - Majalisar dinkin Duniya

Dakatar da Alkalin Alkalai na Najeriya ya sabawa doka ta Duniya - Majalisar dinkin Duniya

Da sanadin babbar kafar watsa labarai ta duniya, Aljazeera, mun samu cewa majalisar dinkin duniya ta yi furuci dangane da hukuncin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na dakatarda alkalin alkalai na Najeriya, Justice Walter Onnoghen.

Babban jami'in na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da alkalin alkalai na kasa, Justice Walter Onnoghen, ya sabawa duk wata doka ta duniya mai kare hakkin da 'yancin bil Adama.

Dakatar da Alkalin Alkalai na Najeriya ya sabawa doka ta Duniya - Majalisar dinkin Duniya
Dakatar da Alkalin Alkalai na Najeriya ya sabawa doka ta Duniya - Majalisar dinkin Duniya
Asali: UGC

Diego Garcia Sayan, ya ce hukuncin shugaba Buhari na dakatar mafi kololuwar alkalin kasa ya sabawa duk wata doka ta duniya mai kare 'yancin bil Adama duba da martaba da kuma iko na cin gashin kai da ya rataya kan hukumar shari'a ta kasa.

Mista Sayan wanda majalisar dinkin duniya ta dorawa nauyin gudanar da bincike kan tabbatar da yiwa dokokin shari'a da'a da kuma kare 'yancin su ya ce, daukar duk wani hukunci kan babban alkali na da babbar nasaba da bibiyar tafarki gami da tsare-tsare da hukumar shari'a mai cin gashin kanta ta tanada.

KARANTA KUMA: Hargitsi yayin taron yakin zabe Buhari, Mutane 3 sun shiga hannu

Kamar yadda shafin jaridar Aljazeera ya ruwaito, Mista Sayan ya ce daukar duk wani hukunci kan alkalai ba tare da bibiyar shimfida ta tsare-tsare da dokoki ba ko kuma jingina da dalilai na shari'a yana cin karo da duk wata doka ta duniya mai kare hakkin da 'yancin hukumar shari'a ta kowace kasa a fadin duniya.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya dauki hukuncin dakatar da alkalin alkalai na Najeriya a ranar 25 ga watan Janairun da ya gabata biyo bayan shawarar wani reshe na hukumar shari'a mai sauraron korafi, inda ya maye gurbin sa da Ibrahim Tanko Muhammad.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel