Wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa

Wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa

- Nasara tana tare da Buhari cewar Oba Akiolu

- Ya bayyana hakan ne a yayin da shugaban kasar yakai ziyara fadar sa a yau a Legas

- Yayi kira ga yan Najeriya dasu cigaba da goya masa baya

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Asali: UGC

A ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu ne shugaban kasa Muhammad Buhari yakai ziyara fadar Riliwanu Akiolu Oba na jihar Legos.

Yakai ziyarar ne dan neman albarka inda Oba yace masa nasara tana tare dakai.

Mr Akiolu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari mutum ne mai magana daya sannan kuma zaiyi nasara a zabe mai zuwa.

Sarakuna tsamo-tsamo a siyasa, an jiyo wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa
Sarakuna tsamo-tsamo a siyasa, an jiyo wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa
Asali: UGC

Akiolu yayi wannan furuci ne a yayin da Buhari yakai ziyarar kamfe masarautar sa bisa zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan nan.

Sarki wanda ya bayyana jindadin sa dama sauran shuwagabannin yankin bisa ga wannan ziyara yace suna jindadin abubuwan da Buharin keyi sannan kuma suna goyan bayansa.

Sarakuna tsamo-tsamo a siyasa, an jiyo wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa
Sarakuna tsamo-tsamo a siyasa, an jiyo wani babban sarki yana kira da ayi Buhari a jiharsa
Asali: UGC

Ya tabbatar wa da Buhari zai kara samun nasara kamar yanda ya samu a shekara ta 2015.

GA WANNAN: 2019: Atiku baya iya cin jihar Ogun - Masana

"Ku bawa Buhari wata damar zakuga yanda Najeriya zata ci gaba"cewar Akiolu.

"Bazamu koma baya ba tunda kana nan insha Allah zaben da za'ayi a 16 ga wannan wata kai ne zaka samu nasarar".

Da yake nasa jawabin Shugaban kasa Muhammad Buhari yace "Nayi matukar farin ciki da wannan furuci naka sannan zan cigaba dayin aiki tukuru"

"Alkawarin da mukayi tun a shekara ta 2015 kasar mu tana bukatar tsaro da kula,idan har babu tsaro to fa babu abinda zamu iya aiwatar wa, amma yanzu mun godewa Allah saboda cigaban da aka samu".cewar Buhari.

Buhari yakai ziyara masarautar da misalin larfe 10:59 na safiyar yau.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel