Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto

Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto

- Jarumar wasar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta caccaka a wajen wasu yan arewa bayan ta saki wasu sabbin hotunanta

- Rahama ta sanya wata riga mai hannu daya wanda ya bayyana daya daga cikin santala-santalan hannayenta a waje

- Don haka yanayin shigar nata bai samu karbuwa ba a wajen wasu yan arewa, da musulman da ke bibiyar shafinta inda suka tunatar da ita irin fushin da Allah ke yi ga masu irin wannan shiga

Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta caccaka a wajen wasu yan arewa bayan ta saki wasu sabbin hotunanta.

Matashiyar yar wasar na burin ganin ta burge sabbin masoyanta sannan ta sanya wata riga mai hannu daya. Da dama sun yaba da kyawun da tayi a hotunan inda suke ta yaba mata da jero sakonnin yabo a gare ta.

Sa dai yanayin shigar nata bai samu karbuwa ba a wajen wasu yan arewa, da musulman da ke bibiyar shafinta inda suka tunatar da ita irin fushin da Allah ke yi ga masu irin wannan shiga. Sun zarge ta da cewar a yanzu rudin duniya ya dibeta shiyasa bata damu da dokokin Allah da manzonsa ba sannan suka gargade ta da ta tuba tun kafin lokaci ya kure mata.

Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto

Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto
Source: Instagram

Wasu kuma sun zarge ta da neman suna da burgewa. Sannan kuma suka yi addu’a kan Allah ya shirye ta ya kuma yafe mata zunubanta.

KU KARANTA KUMA: An kama wani mutum da ke danne yaro dan shekara 13 ta dubura

Ga wasu daga cikin sharhin a kasa:

Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto

Sharhin da wasu suka yi akan shigarta
Source: Twitter

Wasu mazan arewa sun caccaki jaruma Rahama Sadau kan sanya riga mai hannu daya a sabon hoto

Sharhin da wasu suka yi akan shigarta
Source: Twitter

Idan dai za ku tuna a watannin baya ne dai masana'antar Kannywood ta dakatar da jarumar sakamakon yanayin da ta bayyana a cikin bidiyon wani mawaki Classiq.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel