Arangama: Dakarun Sojin Najeriya sun aika da yan Boko Haram 4 zuwa barzahu

Arangama: Dakarun Sojin Najeriya sun aika da yan Boko Haram 4 zuwa barzahu

Dakarun rundunar Sojin Najeriya na 118 da na 119 sun aika da wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram su hudu zuwa barzahu bayan wata zazzafar arangama data faru a garin Malam Fatori, dake kan iyakar Najeriya da Chadi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a daren Asabar, 2 ga watan Janairu a cikin karamar hukumar Abadam ta jahar Borno, yayin da mayakan suka yi kokarin kutsa kai cikin garin Malam Fatori da nufin kaddamar da hare hare.

KU KARANTA: Rundunar soji ta kama 'yan dabar siyasa da muggan makamai, hotuna

Arangama: Dakarun Sojin Najeriya sun aika da yan Boko Haram 4 zuwa barzahu
Boko Haram
Asali: Facebook

Sai dai kamar yadda masu iya magana ke cewa, kifi na ganinka mai jar koma, ashe dakarun Sojin runduna ta 118 da ta 119 suna kallonsu, inda nan take suka taresu, suka dinga antaya musu luguden wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan ta’adda guda hudu.

Haka zalika Sojojin sun raunata yan ta’adda da dama, wadanda suka ranta ana kare babu shiri, kuma a yanzu haka Sojoji sun shiga farautarsu ruwa a jallo, kamar yadda mataimakin daraktan watsa labaru na Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema ya bayyana.

Arangama: Dakarun Sojin Najeriya sun aika da yan Boko Haram 4 zuwa barzahu
Makamansu
Asali: Facebook

Sai dai Kaakakin yace an samu wasu Sojoji da suka jikkata, wanda a yanzu suna samun kulawa, amma yace Sojojin sun kwato bamabamai guda hudu, bindigar mashingon guda daya, alburusai da dama da kuma sauran kayan harba bamabamai.

Daga karshe kaakaki Onyema ya gode ma goyon bayan da rundunar ke samu daga wajen jama’an yankin Borno, sa’annan ya bukaci su cigaba da taimaka musu da bayanan sirri wanda zasu taimaka musu wajen kawo karshe yan ta’adda a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel