Tsafi: Dalilin da yasa ba zamu iya binciken satar kamfai ba - 'Yan sanda

Tsafi: Dalilin da yasa ba zamu iya binciken satar kamfai ba - 'Yan sanda

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ba za ta iya bincikar satar kamfai da akeyi domin asiri da kamfai ba abu ne da za a iya gani a zahiri ba

- Rundunar 'yan sandan ta ce muddin ba an samu aikata wani mugun aiki kamar kisa, yunkurin kasar ko wani abu mai kama da haka ba ba za ta iya gudanar da bincike ba

- Kakakin 'yan sandan Najeriya, Frank Mba ya ce shaye-shayen kwayoyi da rashin ayyukan yi suna daga cikin abubuwan da ke sanya matasa aikata miyagun ayyuka

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ba za ta iya bincikar satar dan kamfan mata da wasu keyi domin yin asiri ba saboda babu wata kwakwarar hujja da ke nuna yiwuwar yin asiri da kamfai.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, Mr Frank Mba ne ya fadi hakan a wata hira da akayi dashi kai tsaye a wani shiri mai suna 'Good Morning Nigeria' a gidan talabijin na kasa NTA a yau Juma'a.

Tsafi: Dalilin da yasa ba zamu iya binciken satar kamfai ba - 'Yan sanda

Tsafi: Dalilin da yasa ba zamu iya binciken satar kamfai ba - 'Yan sanda
Source: UGC

DUBA WANNAN: Rarara da Ado Gwanja sun gwangwaje a wurin kamfen din Buhari

Mba yana amsa tambayoyi ne a kan asiri da mutane ke yi domin yin arziki a dare daya.

Ya ce, "Satar dan kamfai sa sabon abu ne, a baya mu kan samu wasu na kisan kai saboda tsafi amma ba za mu iya bincike a kan abinda ba bu hujja da tabbatar da afkuwarsa ba sai dai idan an samu kisan kai ko yunkurin aikata hakan ko wadansu laifi masu kama da hakan."

Mba ya ce ta'amulli da miyagun kwayoyi ne ke janyo aikata laifuka. Ya yi kira ga matasa su nisanci shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa, "Miyagun kwayoyi su kan gusarwa mutum da tausayi shi yasa za ka ga wasu na kisa da wasu miyagun ayyuka domin suyi kudi. Zamu cigaba da yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi amma muna bawa matasa shawara su dena shan kwayoyi ko kuma su gamu da doka.

"Bamu bincike a kan abubuwan da suka shafi tsafi ko asiri sai dai idan an hada da miyagun ayyuka a ciki. Baya ga rashin ayyukan yi da sauransu abubuwan da muke gani a talabijin da rediyo suna da tasiri a kan matasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel