Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

- Wani magidanci ya kashe matarsa har lahira saboda yana zarginta tana kawo masa gardawa gida idan baya nan

- Magidancin, Jibrin Abu ya ce wannan babban abin kunya ce a al'adarsu shi yasa ya kashe ta domin ya wanke sunansa da na zuri'arsu

- Kafin a kai ga kisar, Abu ya ce ya dade yana gargadinta ta dena amsa wayar gardawa a gidansa amma tayi kunnen uwar shegu da rokonsa

Jami'an Rundunar 'Yan Sandan Najeriya sun kama wani magidanci mai shekaru 32, Jibrin Abu da ake zargin ya kashe matarsa, Victoria Aliyu ta hanyar yi mata mummunan bugu da katako saboda yana zarginta da cin amanar aure.

'Yan sanda da ke aiki da caji ofis na Lapai da ke karamar hukumar Lapai na jihar Neja ne su kayi nasarar kama Abu.

Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure
Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan Muhammad da Onnoghen

Northern City ta gano cewar wanda ake zargin ya yiwa matarsa gargadin cewa ta dena amsa wayar abokanta maza amma sai tayi biris da wannan gargadin na sa.

Abu ya yiwa majiyar Legit.ng bayanin abinda ya faru har ta kai ga kisar Victoria a ranar Talata, "Nayi amfani da katoka ne wurin kashe ta bayan na yi mata gargadi sau da yawa a baya domin ta dena amsa wayar gardawa a gidana.

"Ina zargin mata ta tana bin maza a kauyen mu amma a yayin da muke musayar kalamai sai na kashe ta."

Wanda ake zargin ya kuma ce tsohuwar matarsa 'abin kunya ce ga mata saboda ta bata masa suna a gari.

"Tsohuwar mata na tana kawo maza cikin gidan mu na aure kuma al'adar mu ta hana hakan; shi yasa na kashe ta domin in kare suna na da na gidan mu na daga abin kunya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel