Amnesty Intl: Ana kashe mu a Najeriya amma ba a magana inji Miyetti Allah

Amnesty Intl: Ana kashe mu a Najeriya amma ba a magana inji Miyetti Allah

Mun ji labari dazu cewa kungiyar nan ta Fulani watau Miyetti Allah Wallidira ta na nema Gwamnatin Najeriya ta kori kungiyar Amnesty International mai kokarin kare hakkin Jama’a daga cikin kasar nan.

Amnesty Intl: Ana kashe mu a Najeriya amma ba a magana inji Miyetti Allah
Miyetti Allah tace akwai rashin gaskiya da annamimanci a lamarin Amnesty Int’l
Asali: UGC

Shugaban Makiyayan Fulanin Najeriya na reshen Miyetti Allah Wallidira,, yayi kira na musamman ga gwamnatin tarayya tayi waje da Amnesty International (AI) daga Najeriya sannan kuma ta kama manyan wannan kungiya,

Alhaji Yusuf Musa Ardo wanda shi ne jagoran Miyetti Allah Wallidira na Najeriya gaba daya ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da ministan harkokin wajen kasar nan watau Geoffrey Onyeama a cikin ‘yan kwanakin nan.

Yusuf Musa Ardo yake cewa an soki daukacin al’ummar Fulanin Najeriya a wani rahoto da Amnesty International ta fitar kwanaki. Musa Ardo yace a wannan rahoto an yi wa Fulanin kasar kudin goro da sunan manyan ‘yan ta’adda.

KU KARANTA: Wani Lauya ya karar Gwamnatin Najeriya saboda dakatar da CJN

Kungiyar ta Makiyaya Fulani ta nuna cewa ba za ta amince da wannan cin fuska da aka yi mata ba don haka ta nemi a kori Amnesty International daga Najeriya tun da aikin na ta ya zama son kai da kuma rashin adalci ga mutanen Fulani.

Kwanaki kungiyar Amnesty International tace an kashe dinbin mutane a sanadiyyar rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya. Sai dai Makiyaya Fulani sun ce ba a nemi jin ta bakin su wajen fitar da wannan rahoto domin su kare kan su ba.

Fulanin sun koka da cewa ana kashe jama’an su da-dama a irin su Taraba, Gembu, Numan da jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da kuma Sokoto amma kungiyar ta AI tayi gum kamar ba ayi komai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel