Boko Haram: Mutane a Yobe sun shiga rudanni bayan sojoji sun tsere

Boko Haram: Mutane a Yobe sun shiga rudanni bayan sojoji sun tsere

An kalla mutane biyu ne suka rasu sannan an sace wasu da dama sakamakon afkawar da mayakan Boko Haram su ka yiwa garin Gaidam na jihar Yobe a jiya.

A cewar hukumomin tsaro, 'yan ta'addan sun afkawa garin ne da yamma a cikin motocinsu misalin karfe 5.30 na yammacin Laraba inda suka fara harbe-harbe.

Sun kone gidaje masu yawa sannan su kayi awon gaba da kayayakin abinci.

Wani dan banga ya shaidawa Sahara Reporters cewa mazauna garin sun san cewa 'yan Boko Haram za su kawo harin domin sun aike musu da wasikar gargadi.

Boko Haram: Mutane a Yobe sun shiga rudanni bayan sojoji sun tsere
Boko Haram: Mutane a Yobe sun shiga rudanni bayan sojoji sun tsere
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kiristoci ne suka taimake ni lokacin da musulmi suka juya min baya - Buhari

A yayin da ya ke bayar da labarin abinda ya faru, ya ce, "kamar yadda ka sani, jiya ne ake cin kasuwar garin Gaidam, saboda haka sunyi amfani da wannan damar inda suka afko mana suna ta harbe-harbe. Mutanen gari duk ana shiga rudani. Sun ci galaba a kan sojojin hakan yasa daga bisani suka tsere. An kashe mana mutum biyu sannan wasu da dama sun jikkata. An kuma sace wadansu."

Wani jigo a kauyen da ya nemi a boye sunansa saboda ba a bashi damar yin tsokai a kan lamarin ba ya ce 'yan ta'addan sun fi sojojin yawa sosai hakan yasa suka ci galaba a kansu a garin na Gaidam.

"Sunyi nasarar kone sansanin sojoji da ke Gaidam kuma suka kone motocci masu dauke da bindiga guda biyu. Sun kuma kone wasu gidaje bayan sun sace kayayakin abinci da tufafi.

"Sojojin sun tsere daga garin ne bayan da 'yan ta'addan suka fara cin galaba a kansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel