Da duminsa: Ana can ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Gaidam

Da duminsa: Ana can ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Gaidam

Rahoton da muka samu na nuna cewa a halin yanzu mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari da garin Gaidam da ke jihar Yobe.

Mazauna garin sun shaidawa Daily Trust a yau Laraba cewa 'yan ta'addan sun shigo garin misalin karfe 5.30 na yamma inda suka rika harbe-harbe.

Wani dan garin ya ce 'yan ta'addan sunyi amfani da damar cewa yau ne ake cin kasuwan garin domin afkawa garin.

Da duminsa: Ana can ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Gaidam
Da duminsa: Ana can ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Gaidam
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya sake samun nasara a kan 'yan sanda a gaban Kotu

"Amma saboda sun sanar da mazauna garin cewa za su kawo hari, tuni sojojin Najeriya sun far musu," inji shi.

Ya ce a halin yanzu jiragen yaki masu saukan ungulu guda biyu sun iso garin domin taimakawa sojojin.

Ya ce a halin yanzu ana nan ana musayar wuta tsakanin sojojin da yan ta'addan.

Sai dai kawo yanzu, rundunar sojin na Najeriya ba ta fitar da sanarwa a kan lamarin ba.

Ku biyo mu domin samun karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164