Yanzu Yanzu: Tsohon shugaban PDP da wasu mambobin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a Yobe

Yanzu Yanzu: Tsohon shugaban PDP da wasu mambobin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a Yobe

- Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Lawan Gana Karasuwa, wani dan takarar kujerar Santa, Dr. Mairo Amshi da wasu magoya bayan jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a jihar Yobe

- Masu sauya shekar sun samu tarba daga Gwamna Ibrahim Gaidam a ranar Talata a yayin gangamin APC a yankin Yobe ta Arewa, a garin Gashua

- Karasuwa ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyarsu ne zuwa APC duba ga tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a dukkan matakan gwamnati a fadin kasar

Wani tsohon shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Lawan Gana Karasuwa, wani dan takarar kujerar Santa, Dr. Mairo Amshi da wasu magoya bayan jam’iyyar sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All progressive Congress (APC) mai mulki a jihar Yobe.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga Gwamna Ibrahim Gaidam a ranar Talata, 22 ga watan Janairu a yayin gangamin APC a yankin Yobe ta Arewa, a garin Gashua.

Yanzu Yanzu: Tsohon shugaban PDP da wasu mambobin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a Yobe
Yanzu Yanzu: Tsohon shugaban PDP da wasu mambobin jam’iyyar sun sauya sheka zuwa APC a Yobe
Asali: UGC

Da yake jawabi a taron, tsohon shugaban PDP ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyarsu ne zuwa APC duba ga tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a dukkan matakan gwamnati a fadin kasar.

Da farko, Gwamna Ibrahim Gaidam ya shawarci mabiya jam’iyyar da masu sauya sheka da su mutunta doka da ra’ayin jam’iyyar da kuma aiki don nasarar ta a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Magajin Aminu Kano, Khalifa Hassan Yusuf ya rasu yana da shekara 83

Hakazalika, dan takarar gwamna na APC a jihar, Mai Mala Buni yayi alkawarin ci gaba da gina ayyukan ci gaba a jihar.

Ya yi kira ga mutanen yankin, Yobe da kasar da su fito kwansu da kwarkwatansu don zabar dukkanin yan takarar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng