Yanzu Yanzu: Magajin Aminu Kano, Khalifa Hassan Yusuf ya rasu yana da shekara 83

Yanzu Yanzu: Magajin Aminu Kano, Khalifa Hassan Yusuf ya rasu yana da shekara 83

- Allah ya yi wa Khalifa Hassan Yusuf (Galadiman Damaturu) rasuwa bayan doguwar jinya

- Marigayin ne ya gaji Malam Aminu Kano a matsayin shugaban jam’iyyar Peoples redeemption Party (PRP)

- Khalifa Hassan ya rasu ya bar matan aure hudu, yara 20 da jikoki 55

Wani jigon kasar, Khalifa Hassan Yusuf (Galadiman Damaturu), wanda ya gaji Malam Aminu Kano a matsayin shugaban jam’iyyar Peoples redeemption Party (PRP), ya rasu.

Dan marigayin, Yusuf Hassan Yusuf, ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ga jaridar Daily Trust a yau Laraba, 23 ga watan Janairu.

Yanzu Yanzu: Magajin Aminu Kano, Khalifa Hassan Yusuf ya rasu yana da shekara 83
Yanzu Yanzu: Magajin Aminu Kano, Khalifa Hassan Yusuf ya rasu yana da shekara 83
Asali: UGC

Yace marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri bayan dogon jinya na cutar daji.

A cewarsa, za a mika gawar mariyagayin gidansa da misalin 8:30 na safe, sannan za a binnesa daidai da koyarwar addinin Musulunci a gidan nasa da misalin 11:00 na safe.

KU KARANTA KUMA: Yayi matukar wahala aiki tare da tsohon IGP – Inji Minista Dambazau bayan ritayan Ibrahim Idris

Marigayin ya rasu ya bar matan aure hudu, yara 20 da jikoki 55.

Hassan Yusuf ya kasance dan taarar shugaban kasa a jam’iyyar People’s Redemption Party a shekarar 1983 lokacin da yayi takara da marigayi Shehu Shagari, marigayi Nnamdi Azikiwe, marigayi Cif Obafemi Awolowo da marigayi Waziri Ibrahim.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng