Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito

Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito

- Miyyeti Allah tace Atiku na amfani da matsalar yan Fulani wajen yin kamfen dinsa

- Kungiyar tace tsohon shugaban kasa ba Bafulatani bane

- An tattaro cewa Atiku yace Buhari ba Bafulatani bane

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore Fulani ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ba Bafulatani bane.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Saleh Alhassan wanda ya kasance babban sakataren kungiyar na kasa na martani ne ga ikirarin Atiku na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba Bafulatani usuli bane.

A wani gangami a igawa, an tattaro inda Atiku yace: “Bafulatanin usuli ba zai efa dan uwansa a cikin kangin talauci ba kamar yadda yake faruwa a yanzu a karkashin gwamnatin All Progressives Congress."

Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito
Atiku ba Bafulatani bane – Miyetti Allah ta bayyana daga inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito
Asali: Facebook

Alhassan yace don Atiku na yaren Fulatanci ba yana nufin shi Bafulatani bane.

Yace: "Batun gaskiya shine, a wurare da dama a jihar Adamawa, suna yaren Fulatanci. Don Atiku ya iya Fulatanci ba yana nufin shi Bafulatani bane.

"Idan ka kalli kirar Atiku, baya dauke da siffar Bafulatani. Kana kallon Atiku ka ga dan kabilar Bantu. Ba dan kabilar Sudan bane.

KU KARANTA KUMA: Kamfen: Yakin neman zaben Atiku a jihar Imo ya yi armashi (hotuna)

"Hakazalika ba mu san kawu Atku ba kuma dukkanin Fulani sun san kawunnansu. Kun taba ganin kawun Atiku? Ikirarinsa na cewa usulinsa Fulani ne ba tabbass domin babu wanda ya san kawunnansa. Kasancewar Buhari Bafulatani babu kokwanto. Mahaifinsa ya kasance Ardo, shugaban Fulani. Din haka ina ganin wannan ba wani abu bane".

Jigon Fulanin yace sun yi watsi da Atiku ne a zabe saboda baya "baya daukar matsalolinmu a matsayin nasa" inda ya kara da cewa dan takarar na PDP na son "amfani da matsalolinsu wajen yin kamfen da su."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng