An lakada wa wani mutun duka bayan an kama shi yana cin burodi da kashi

An lakada wa wani mutun duka bayan an kama shi yana cin burodi da kashi

- Wasu dandazon matasa sun lakada wa wani mutun dukan tsiya bayan kama shi yana cin burodi da kashin mutum

- Ana zargin da kasancewa mutumin mamba a cikin wata kungiyar asiri mai cin naman mutane

- Mutumin dai yayi tsirara ne a lokacin da yake cin burodi da kashin a sanyin safiya

Wasu dandazon matasa sun lakada wa wani mutun dukan tsiya bayan kama shi yana cin burodi da kashin dan adam a jihar Ekiti.

Jama’ar yankin da abin ya faru, sun shaida wa ‘yan sanda cewa, mutumin mamba ne a cikin wata kungiyar asiri mai cin naman mutane, abin da ya sa matasan suka kona wani sashi na jikinsa kafin daga bisani suka kashe shi har lahira.

An lakada wa wani mutun duka bayan an kama shi yana cin burodi da kashi
An lakada wa wani mutun duka bayan an kama shi yana cin burodi da kashi
Asali: Depositphotos

Rahotanni na cewa, wata tsohuwa ce ta fara gano mutumin wanda ya yi tsirara a yayin da yake cin burodi da kashin a sanyin safiyar ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: NLC ta ki amincewa da N27,000 a matsayin mafi karancin albashi

Gabanin kashe shi, mutumin ya ambaci sunayen wasu limaman coci da ya ce yana da alaka da su, lamarin da ya sa gungun matasan kutsa cikin harabar wani coci domin neman daya daga cikin limaman, amma tuni ya ari na kare duk da dai an ce, an cafke shi a wata mahadar hanyoyi.

Tuni dai matasan suka rusa cocin da limamin ke jagorantar masu ibada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng