Chiroki bai tallafa wa kowa a Kannywood ba – Ali Nuhu

Chiroki bai tallafa wa kowa a Kannywood ba – Ali Nuhu

- Jarumin wasan Hausa, Ali Nuhu ya mayar da martani akan ikirarin cewa masana'atar Kannywood ta watsar da Chiroki

- Ali ya kalubalanci masu korafi da su bayyana masa mutanen da abokin sana'arsa da Chiroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo

- A wata hira da aka yi da Chiroki a tashar Arewa24, inda ya bayyana cewa yan kannywood sun yi watsi dashi bayan an daina sanya shi a fina-finai, don haka yake kulla kunun aya yana yawon talla a gari

Fitaccen jarumin fina-finan Kannywood wanda aka fi sani da sarki mai Kannywood mai sangaya, Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana'arsa Bashir Bala, wanda aka fi sani da Chiroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo.

Wani mai amfani da shafn twitter mai suna Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadi kan yadda jaruman Kannywood suka yi watsi da Chiroki duk da cewa yana tsananin bukatar taimako.

Hakan ya biyo bayan wata hira da aka yi da Chiroki a tashar Arewa24, inda ya bayyana cewa yan kannywood sun yi watsi dashi bayan an daina sanya shi a fina-finai, don haka yake kulla kunun aya yana yawon talla a gari.

Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai

KU KARANTA KUMA: TraderMoni: Osinbajo ya fadi dalilan da yasa Obasanjo ke sukar shirin

Sai dai a jerin martanin da Ali Nuhu ya yi wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Chirokin ya bai wa Kannywood.

"Zan yi maka tambaya: lokacin da Chiroki yake tashe wa ya taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa masu shirya fim? Ya kamata mu san abin da muke yi."

Ya ce bai kamata a rika yi wa 'yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel