Dan Allah ka je ka huta – Obasanjo ya sake caccakar Buhari, yace shugaban kasar baida lafiya

Dan Allah ka je ka huta – Obasanjo ya sake caccakar Buhari, yace shugaban kasar baida lafiya

- Cif Olusegun Obasanjo ya nemi a bari shugaba Muhammadu Buhari ya je ya huta

- Tsohon shugaban kasar ya yi ikirarin cewa Buhari baida lafiya sannan cewa akwai bukatar hana shi sake mulkar kasar

- Yace damokradiya ta bayar da damar maye gurbi da wani da wani

Karo na biyu a kasa da sa’o’i 48, Cif Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya caccaki shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari inda ya bukaci da ya je ya huta.

Obasanjo ya ce lallai shugaba Buhari bai da isasshen karfin rike al’amuran Najeriya bayan 2019.

Jaridar The Cable ta rahoto daga shafin BBC harshen Yarbawa, cewa Obasanjo yace Buhari “baida lafiya a ruhi, jiki da kuma tunaninsa.

Dan Allah ka je ka huta – Obasanjo ya sake caccakar Buhari, yace shugaban kasar baida lafiya
Dan Allah ka je ka huta – Obasanjo ya sake caccakar Buhari, yace shugaban kasar baida lafiya
Asali: Twitter

Ya yi roko cewa Buhar na bukatar hutu saboda wani mutun ya dauki ragamar mulkin kasar.

A cewar Obasanjo, a duk lokacin da mutane suka yi masa korafin cewa ba lallai ne mutun na gaba yayi kokari fiye da hakan ba, yakan fada masu cewa damokradiya ta bayar da damar maye gurbi da wani.

KU KSARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya daukar ma mutanen jihar Borno babban alkawari

A baya mun ji cewa Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Obasanjo koda kasar Najeriya kacokan mutun ya sata indai dan APC ne toh za a wanke masa laifinsa kuma babu abunda za a yi masa.

Yace amma da za a ce mutum ya saci naira 10 indai ya soki Buhari da gwamnatinsa koda shekara 15 da ta wuce ne ya saci kudin sai an nemi ya dawo da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng