Atiku zai gana da yan majalisar Amurka

Atiku zai gana da yan majalisar Amurka

- Tsohon mataimaki shugaban kasa Atiku Abubakar ya isa kasar Amurka

- A yanzu haka yana a hanyarsa ta zuwa Washington don ganawa tare da manyan tawagar majalisar Amurka

- Atiku zai kuma yi ganawa da dama da shugabanni yan kasuwa, manyan jami’an gwamatin Amurka, shugabanni masu tarin sani da kuma ya Najeriya mazauna kasar waje

Tsohon mataimaki shugaban kasa Atiku Abubakar ya isa kasar Amurka sanan yana a hanyarsa ta zuwa Washington don wata ganawa tare da manyan tawagar majalisar Amurka wadanda ke da matsanacin kula da damuwa akan makomar damokradiyar Najeriya.

Tawagar na neman shawarar Atiku akan hanya mafi inganci da Amurka za ta bi wajen taimakawa Najeriya do tabbatar da damokradiya a dukkan matakai da kuma tabbatar da cewa an ba ra’ayin mutane muhimmanci a koda yaushe.

Atiku zai gana da yan majalisar Amurka
Atiku zai gana da yan majalisar Amurka
Source: Twitter

Mai girma dan takarar zai yi ganawa da dama da shugabanni yan kasuwa, manyan jami’an gwamatin Amurka, shuabanni masu tarin sani da kuma ya Najeriya mazauna kasar waje.

Kun ji cewa idan za’a tuna an dade ana yamadidin cewar Atiku ba zai iya taka kafarsa ya shiga kasar Amurka ba sakamakon nemansa da suke yi ruwa a jallo da nufin kama shi a kan zarge zargen rashawa.

KU KARANTA KUMA: Gungun Kungiyoyi da Mutanen da za su yi zama da Atiku Abubakar a Amurka

Amma sai ga shi a ranar Alhamis 17 ga watan Janairu Atikun ya isa kasar Amurka, tare da daraktan yakin neman zabensa, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, inda ma suka sauka a otal din shugaban kasar Amurka, Trump Hotels.

Wannan ziyara ta Atiku ta tayar da kura a farfajiyar siyasar Najeriya, musamman ta yadda yan Najeriya da dama suna da yakinin tabbas idan Atiku ya shiga Amurka sai Amurka ta kamashi, don haka magoya bayansa ke musu dariya a yanzu, kuma martabarsa ta karu a idonsu.

Sai dai jami’i mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibeh ya bayyana cewa iya kwanaki biyu kacal Atiku zai kwashe a kasar Amurka tare da tawagarsa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaitoshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng