Kungiyar 'yan kasuwa ta yaba da manufar Atiku a kan kasuwanci
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP da matamakinsa Alhaji Atiku Abubakar da Mista Peter Obi, sun halarci wani taro tare da yan kasuwa a ranar Laraba, a otel din Eko. Taken taron shine ‘Getting Nigeria’s Economy Working: A Pragmatic Approach’ wanda ke magana ne akan tattalin arzikin kasar. Tun da fari dai dan takarar ya kaddamar da akalar kamfen dinsa ne akan samar da ayyukan yi. A baya dai ya bayyana cewa zai samar da ayyuka 45, 000 a matsayinsa na dan kasa mai dogaro da kai. Ga yan Najeriya da dama, wannan kadai ya isa hujjar da za a mika ragamar mulkin kasar a hannunsa, duba ga cewa dukkanin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a yanzu na da nasaba da rashin ayyukan yi.
Sai dai kuma Opeyemi Agbaje, mai gabatarwa, ya so sanin yadda matsayarsa take a wajen samar da wannan shiri. Dalili kuwa shine gwamnatoci sun karyata manufofinsu da shelar da suke yi a baya. Akan haka Atiku yace, “Wannan ba shine daftarin manufa na farko da nake kafawa ba. Ina so na baku tabbacin cewa ni da kaina na kasance cikin shirya dabarun. Na kuma yi aiki tare da manyan kwararru.” Da wannan amsa, mai gabatarwar dsa sauran mambobin kungiyar sun fahimci cewa dan takarar na da shirye-shirye na kansa ga tattalin arzikin Najeriya.
Atiku ya ci gaba akan kwarewarsa game da manufofin, “A 2007 lokacin da naso yin takara, nayi aiki tare da kwararru don don samar da babban shiri na Niger Delta. Lokacin da na fadi zabe, na mika shi ga Yaradua. Wannan takarda ya yi sanadiyar garambawul da kuma samar da ma’aikatar Niger Delta.”kan nasara da ci gaban tattalin arziki a lokacin da yake kan mulki, Atiku ya bayya cewa sirrin da ke tattare da hakan shine cewa a koda yaushe yana haduwa da yan kasuwa sannan a sanadiyar hakan yake sanin bukatunsu. Wannan ya yi sanadyar ci gaban tattalin arziki da 7%, sabanin yadda yake a yanzu ci gaba da 1.8%.
Akan babban gibin da kasar ke fuskanta ta wajen ababen more reayuwa, Mista Obi yace, “Idan hara a gyara Najeriya toh sai hukumomi masu zaman kansu sun yi jagoranci. Hakan ne ke faruwa a wasu wuraren. Gwamnati bata da karfin samar da ababen more rayuwar da muke bukata a yanzu.” Mista Obi ya bayyana cewa hikimar barin gwamnati ta rike fannin ababen more rayuwa na tattare da matsalar bashin tattalin arziki wanda hakan ke rage kudaden da ya kamata a kashe a fannin ilimi da lafiya.
Akan ayyuka, wanda shine kalubale a kasar, duba ga cewa shekarar 2018 kasar ta fuskanci rasa ayyuka 20.m, Mista Obi ya bayyana cewa a China na amfani da kananan sana’o’i wajen samar da ayyukan yi. Ya baana cewa kananan sana’o’i ya taimaka da kaso 60% a tattalin arzikin China sannan ya kamata Najeriya ta koyi darasi daga gare su. Da farko ya bayyana cewa yana kwatanta China da Najeriya saboda suma sun taa rashin kudi kamar Najeriya, duk da cewar sunma fi Najeriya yawan mutane.
Hakazalika, shahararriyar yar wasa, Onyeka Onwenu ta tambayi shirin da Atiku ke yiwa mata. Akan haka Atku ya bayyana cewa yana da shirin ba mata kaso 30% na mukamai sannan kaso 40% ga matasa, runda sune suka hada kaso 70% na al’umman kasar. Hakan na daga cikin abubuwan da yake yi a matsayinsa na wanda ya mallaki kamfanoni masu zaman kansu. Yace 45,000 na ma’aikata da ke karkashinsa, 70% mutane ne yan shekara 25 zuwa 30, wanda rabinsu mata ne. Sannan kuma ya bayar da umurnin cewa 80% na bashi daga bankunan da yake gudanarwa su kasance mata ne ke cin moriyarsu.
KU KARANTA KUMA: Karya ne bamu saki katunan zabe ga gwamnonin APC ba – INEC
Peter Obi ya fayyace komai akan daukar ilimi a matsayin wani wajen zuba jari, maimakon wajen kashe kudi. Ya bayyana cewa kamfanonin da suke da ilimi, suna samun kudi fiye da Najerya. Bugu da kari, Atiku ya bayyana cewa sun gabatar da dokar samun tushen ilimi a lokacin da yake a matsayin mataimakin shugaban kasa. Wannan dokar ta sa an wajabta cewa sai yara sun samu ilimin firamare. Don haka, yana shirin ba fannin ilimi muhimmanci na musamman, tunda shine abunda Najeriya ke bukata. Akan dukkanin wadannan abubuwa, shirin gwamnatin Atiku Abubakar da Peter Obi ne abun dba. Rage girma da tsadar gwamnati shine hanya na farko da za a cimma nasara a shugabanci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng