Dandazon jama’a sun lamunce wa Buhari a Kogi – Jigon APC

Dandazon jama’a sun lamunce wa Buhari a Kogi – Jigon APC

- Mataimakin shugaban kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC a Kogi yace shugaba Buhari za yi gagarumin nasara a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu

- Mista Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa Buhari yayi matukar kokari kuma ya cancanci samun kuri’u masu yawa daga dukkanin yan Najeriya

- Ya kuma shawarci masu zabe da su guje ma duk wani rikici don ba zai fisshe su ba

Mista Kingsley Fanwo, mataimakin shugaban kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC a Kogi, a ranar Laraba, 16 ga watan Janairu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari za yi gagarumin nasara a zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu.

Fanwo ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a gefen gangamin dan takarar shugaban kasa na APC da aka gudanar a Lokoja, cewa Buhari yayi matukar kokari kuma ya cancanci samun kuri’u masu yawa daga dukkanin yan Najeriya.

Fanwo wanda ya kuma kasance Darakta Janar na labara Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa tashar jirgin kasa na Itakpe zuwa Warri na aka gyara yana daya daga cikin abubuwanda Buhari yayi wa mutanen Kogi.

Dandazon jama’a sun lamunce wa Buhari a Kogi – Jigon APC
Dandazon jama’a sun lamunce wa Buhari a Kogi – Jigon APC
Asali: Facebook

Ya kuma shawarci masu zabe da su guje ma duk wani rikici, cewa “babu alkharin da rikici zai yi mana a zabe a kwace jam’iyya mutum yake.”

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa nake neman Karin shekaru 4 akan mulki – Buhari

Mista Ademola Bello-Destinu, dan takarar dan majalisar dokoki na jiha a APC ya bayyana cewa tarin jama’ar da suka halarci gangamin shugaban kasar alamu ne na cewa yan Najeriya sun san cewa Buhari ne zabin Kogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng