Ba cuta ba cutarwa: Karanta don jin nawa zaka biya idan zaka yi sabon fasfo

Ba cuta ba cutarwa: Karanta don jin nawa zaka biya idan zaka yi sabon fasfo

A cikin makonnan ne gwamnatin Najeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samar da wani sabon fasfo da aka inganta wanda yan Najeriya zasu dinga amfani da shi wajen fita kasashen waje.

Legit.ng ta ruwaito wannan sabon fasfo zai yi aiki na tsawon shekaru goma, wanda hakan ke nufin bayan duk shekara goma ana bukatar mutum ya sabuntashi, aikinsa ya kare, kamar yadda shugaban hukumar kula da shige da fice, Mohammed Babandede ya bayyana.

KU KARANTA: Gangamin fasa kwalaben giya 60, 000 a Kano ya dauki hankalin yan Najeriya

Ba cuta ba cutarwa: Karanta don jin nawa zaka biya idan zaka yi sabon fasfo
Sabon fasfo
Asali: Facebook

Babandede ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da hukumar ta kaddamar da sabon fasfon a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa, inda ta fara yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osibanjo.

Dayake ana gudun kada yan Najeriya su fada hannun macuta da zasu nemi makudan kudade daga wajensu da nufin sama musu wannan fasfo, hukumar kula da shige da fice ta sanar da farashin duka samfurin fasfon kamar haka;

Fasfo mai shafuka 32 da zai gama aiki bayan shekara 5 = Naira 25,000 ko dala 130

Fasfo mai shafuka 64 da zai gama aiki bayan shekara 5 = Naira 35,000 ko dala 150

Fasfo mai shafuka 64 da zai gama aiki bayan shekara 10 = Naira 70,000 ko dala 230

Sai dai kaakakin hukumar kula da fice na Najeriya, Sunday James ya bayyana cewa fitowar sabon fasfon ba wai zai hana amfani da tsohon fasfon bane ga masu mallakarta, don haka duka fasfon zasu yi aiki tare.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindiga sun kai farmaki ga ofishin jami’an kula da shige da fice watau Immigration, dake cikin karamar hukumar Kankara ta jahar Katsina, inda suka banka ma ofisoshinsu da dakunansu wuta.

A wani kaulin kuma, majiyarmu ta ruwaito wai wani jami’in immigration ne ya harbi wani direban motar haya yayin da yaki tsayawa a shingen bincike saboda birkinsa ya shanye, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.

Mutuwar wannan bawan Allah ne ta harzuka sauran abokansa direbobi dake aiki a tashar Maje dake kauyen Maje suka yi kwamba, suka tasan ma shingen binciken, anan ne suka tarwatsa jami’in hukumar Immigration, suka kuma banka ma ofishinsu da dakunansu wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel