Kundin tarihi: Yadda Manjo Kaduna ya kashe Sardauna da matar sa a 1966 - Gidado Idris

Kundin tarihi: Yadda Manjo Kaduna ya kashe Sardauna da matar sa a 1966 - Gidado Idris

Marigayi Gidado Idris, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya mutu yana da shekaru 82 ba tare da ya taba rubuta littafi a rayuwar sa ba. Amma a wata hira da jaridar Daily Trust tayi da shi yayin murnar cikar sa shekaru 80 a duniya a shekarar 2015, ya bayar da tarihin rayuwar sa a cikin tsawon shekaru 35 da ya yi yana aikin gwamnati.

Idris, wanda ya kasance sakataren Sardauna, ya fayyace yadda Manjo Kaduna Nzeogwu ya kashe Firaministan yankin arewa a wani yunkurin juyin mulki na ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966.

Kundin tarihi: Yadda manjo Kaduna ya kashe Sardauna da matar sa a 1966 - Gidado Idris
Kundin tarihi: Yadda manjo Kaduna ya kashe Sardauna da matar sa a 1966 - Gidado Idris
Asali: Twitter

"A yammacin ranar 14 ga watan, ana gobe za a kashe shi, da misalin karfe 8:00 na dare Abubakar Tafawa Balewa ya kira ya ce yana son magana da Sardauna. Na hada su a waya suka yi magana. Bayan sun kammala magana sai Sardauna ya kira ni ya tambaye ni a kan bashin da ake binmu a shagon da muke karbar kaya.

DUBA WANNAN: Kamfen: Hotunan irin tarbar da aka yiwa Buhari a jihar Kogi

"Washegari, ranar da za a kashe shi, da rana ya kira ni tare da mai tsaron lafiyar sa, Aliyu Kangiwa, ya umarci mu je mu gano sabon ofishin da ake gina masa. Tun kafin tafiyar mu an sanar da shi cewar Samuel Akintola, Firemiyan yankin yamma, zai ziyarce shi. Duk wannan na faruwa ne a cikin watan azumi.

"Bayan Akintola ya zo sai yake shaidawa Sardauna cewar sojoji na shirin yin juyin mulki, sai Sardauna ya fada masa cewar yana da labari amm ya bar komai hannun ubangiji.

"Sai Akintola ya ce masa yazo da jirgi, zasu iya amfani da shi domin guduwa koda Nijar ne amma sai Sardauna ya ki amincewa da hakan tare da shaidawa Akintola cewar ba zai iya guduwa ya bar mutanensa ba, sannan ya shawarci Akintola ya koma ya fada wa jama'ar sa abinda ya sani dangane da juyin mulkin da ya ce ya tabbatar sojoji na shiryawa.

"Bayan tafiyar Akintola mun koma gida mun sha ruwa Dankwairo yazo yana yiwa Sardauna wakoki sai ga Alhaji Ali Akilu, sakataren gwamnatin yankin arewa, da M. D Yusuf, kwamishinan 'yan sanda, da Birgediya Janar Samuel Ademulegun, da ganinsu sai Sardauna ya mike suka shige ofis tare dasu.

"Bayan sun tafi sai Sardauna ya ce zai je ya kwanta, lokacin har 11:30 na dare ta wuce. Ganin haka sai muka yanke shawarar mu tafi gida mu kwanta," a cewar Idris.

Tsohon sakataren na Sardauna ya ce, ashe tun kafin fitowar su sojoji sun kewaye gidan Sardauna.

"Abubakar Umar, wani sakataren na Sardauna daga Kano, ya ga duk abinda ya faru ta tagar dakin saukar baki da yake ciki.

"Nzeogwu ya fito da Sardauna da matansa da masu aiki, sannan ya umarci su nuna masa waye Firemiya ko ya kashe su gaba daya.

"Sardauna da kansa ya mike ya ce 'nine wanda kuke nema'. Lokacin da suke kokarin harbe shi ne sai daya daga cikin matansa ta ce sai dai a kashe su tare. Tare aka harbe su, rungume da juna. Nan suka tafi suka bar gawar su," kamar yadda Idris ya fada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng