Ba za ku iya tursasa Buhari zuwa wajen muhawarar yan takarar shugaban kasa ba – Sanata Sani
- Sanata Shehu Sani ya fada ma ýan Najeriya da suka ce lalla sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci muhawarar yan takarar shugaban kasa da za a yi cewa ba dole bane sai shugaban kasar ya shiga muhawarar
- Sani yace so kawai ake a tozarta shugaban kasar ta hanyar yin raddi da abunda ya fadi
- Yace shugaban kasar ya dade yana Magana don haka a cewarsa wannan ma ya isa
Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar ya fada ma ýan Najeriya da suka ce lalla sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci muhawarar yan takarar shugaban kasa da za a yi a ranar 1 ga watan Jaianru cewa ba za a iya tursasawa shugaban kasar shiga muhawarar ba.
Sani wanda ya bayyana hakan a shafin twitter yace shugaban kasar ya dade yana Magana don haka a cewarsa wannan ma ya isa. Yace kawai mutane na son tozarta shugaban kasar ne ta hanyar raddi akan abun da ya fadi.
A baya mun ji cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki tace babu wani abu na musamman game da muhawarar yan takarar shugaban kasa, cewa dan takararta na shugaban kasa, Shugaba Muhammadu Buhari na iya kin halarta idan har yaga akwai wasu hanyoyi da zai iya zantawa da yan Najeriya.
Jam’iyyar wacce tace za ta yanke shawarar ko Buhari zai halarci muhawarar da aka shirya a karshen makon nan ta bayyana cewa muhawara na daya daga cikin hanyoyin da yan takarar shugaban kasa ka bi wajen zantawa da jama’a akan shirinsu ga kasar idan aka zabe su.
KU KARANTA KUMA: Wasu hadiman Dankwambo sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
Da yake jawabi ga manema labarai, Mallam Lanre Issa-Onilu, sakataren jam’iyyar na kasa yace APC za ta duba sauran hanyoyi da shugaba Buhari zai iya amfani da shi wajen zantawa da yan Najeriya, inda ya kara da cewa babu wani abu idan har tana ganin muhawarar ba wannan kadai ne hanyar ba.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng