Dalilin da yasa na bar PDP zuwa APC – Sanata Umar Kumo
- Wani dan kashenin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sauya sheka zuwa APC
- Sanata Umar Kumo wanda ya kasance dan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa PDP na so ta wofantar da harkar siyasarsa ta hanyar mayar da shi ba kowan-kowa ba
- Ya sha alwashin cewa tunda ya sauya sheka zuwa APC, toh lallai sai ta kare ma PDP dad an takarata a zabe mai zuwa
Kudirin takarar shugabancin dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya hadu da cikas a yankin arewa maso gabas yayinda wani babban jigon jam’iyyar wanda ya kasance dan kashenin tsohon mataimakin shugaban kasar, Sanara Saidu Umar Kumo ya sanar da batun sauya shekarsa daga jam’iyyar zuwa All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Yayinda yake tabbatar da sauya shekar nasa a wani hira da manema labarai ta wayar tarho a Gombe a ranar Talata, 15 ga watan Janairu, Sanata Umar Kumo wanda ya kasance dan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa PDP na so ta wofantar da harkar siyasarsa ta hanyar mayar da shi ba kowan-kowa ba a abubuwan da ya shafi zaben 2019.
Ya sha alwashin cewa tunda ya sauya sheka zuwa APC, toh lallai sai ta kare ma PDP dad an takarata a zabe mai zuwa.

Asali: UGC
A cewarsa, “Ba a wasa da ingarman doki a harkar siyasa wanda ke da dubban mabiya sannan kuma ya bayar da gagarumin gudunmawa a jam’iyyar ta hanyar mayar da shi ba komai ba a yayinda ake gina lamarin zabe.”
Tsohon sakataren jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) kuma tsohon mai ba marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar’adu shawara ya bayyana cewa kwanan nan zai yanki katin zama dan jam’iyya a APC a yankinsa na karamar hukumar Akko don tabbatar wa da duniya cewa ba da wasa ya zo ba.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Na samu umurni daga hedkwata cewa kada na mika mukami na ga Egbetokun – Edgal Imohimi
Yayinda yake jadadda goyon bayansa ga APC, Sanata Umar Kumo ya bayyana cewa AP-C ce jam’iyyar da za tayi wa Najeriya aiki sosai yayinda shugaban kasa Buhari ya kasance dan takara guda da ya kafa tarihi na martaba da gaskiya tare da son ci gaban Najeriya zuwa mataki na gaba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng