Allah ya yiwa shahararren jarumin Kannywood Sani SK rasuwa

Allah ya yiwa shahararren jarumin Kannywood Sani SK rasuwa

Labari da ke iso mana ya nuna cewa Allah ya yiwa Shahararren ɗan wasan Hausa na Kannywood Sani Garba S.K rasuwa.

An tattaro cewa jarumin ya rasu ne bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya. Mun samu labarin rasuwar nasa ne a shafin Jaridar Dimokuradiyya.

Sai dai kuma an samu sabanin rahoto akan mutuwar jarumin, domin wasu na ganin cewa labarin kagaggen labari ne cewa yana nan da ransa a asibiti inda yake jinya.

Allah ya yiwa shahararren jarumin Kannywood Sani SK rasuwa
Allah ya yiwa shahararren jarumin Kannywood Sani SK rasuwa
Asali: UGC

Jarumin ya dade a harkar fim kuma ya fito a cikin fina-finai da dama kafin mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Alhaji Shehu Shagari rasuwa

Allah ya jiƙan sa da rahama, yasa Aljannah ce makomarsa, mu kuma idan tamu tazo yasa mu cika da imani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel