Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a kasar Zimbabwe

Farashin Man Fetur ya yi tashin doron zabuwa a kasar Zimbabwe

Za ku ji cewa, daga mafara ta yau ranar Lahadi, an samu tashin doron zabuwa linki bayan linki na farashin man fetur da makamashin gas inda aka samu doriyar kaso 240 bisa 100 a kasar Zimbabwe da ke nahiyyar Afirka.

Gabanin ranar yau ta Lahadi, farashin lita guda ta man fetur bai wuci dalar Amurka 1.32, Naira 481 kenan a kudin Najeriya. A yanzu gwamnatin kasar ta koma sayar da ita a kan Dalar Amurka 3.31 na kowace lita guda, da farashin yayi daidai da Naira 1,204 a kudin kasar nan.

Najeriya na ci gaba da sayar da lita guda ta man fetur akan farashin Naira 145 tun bayan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbi ragamar jagorancin kasar nan a hannun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa
Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa
Asali: UGC

Al'ummar Najeriya na ci gaba da korafi gami da koken yadda gwamnatin Buhari ke ci gaba da sayar da lita guda ta man fetur a kan naira 145 duk da kasancewar kasar nan daya daga cikin kasashen duniya ma su arziki na man fetur da ma'adanan sa.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, shine ya bayar da sanarwar hakan a daren jiya na Asabar tare da bayyana cewa, an samu hauhawa na farashin man fetur sakamakon takaddamar darajar kudin kasar da ta yi daidai da kudin kasar Amurka.

KARANTA KUMA: Kudan Zuma ya tashi al'ummar garin Gunsun na jihar Filato

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin Zimbabwe ta kara farashin man fetur a sakamakon yunkuri da kuma shirye-shiryen ta na cin gashin kanta ta fuskar buga samfurin kudin ta da karan kanta nan da watanni 12 masu gabatowa a madadin dogaro da kasar Amurka.

Ministan tattalin arziki na kasar, Mthuli Ncube ya ce, ci gaba da amfani da samfurin kudi irin na kasar Amurka ba zai kawo karshen matsalolin tattalin arziki da kasar ke ci gaba da fuskanta a halin yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel