Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido

Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido

- An daure shi shekaru biyu a kurkuku

- Matashi ne dan shekaru 25 a Badun

- Alkaliyar tace zai iya biyan N100, 000 ya huta da dauri

Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido
Hukumci: An kulle matsashin da ya tsiyayar wa da makwabcinsa ido
Asali: Depositphotos

Bayan da kotun jihar Oyo a birnin Badun, ta tabbatar Taiwo Ojewola ya caka wa makwabcinsa icce a ido, tace za'a daure shi shekaru biyu da kwakwaran matakin aikin wahala.

Sai dai kotun kuma, tayi masa sassaucin muddin ya biya N100,000 to za'a sake shi ya koma gida, ga alama kuwa, bashi da wannan kudi.

Alkaliyar, Mrs Basirat Gbadamosi, tace a nemo sauran mutum biyu da suka taya matashin wannan aiki na bugun makwabci Mr Sunday David, wanda suke gidan haya daya.

DUBA WANNAN: Sanatocin da suka tsaya wa Nnamdi Kanu sun kasa biyan N100m ta kariya bayan ya tsere

Shi dai Mr Sunday David, ya rasa idon nasa gaba daya bayan da matashin dan shekaru 23 ya caka masa itace, bayan wata 'yar hayaniya ta hado su.

Abin haushin dai shine, muddin matashin ya iya biyan kotu wadannan kudade, to kuwa ya sha, sai dai kuma babu wanda zai iya biyan Mr Sunday David kudin idanunsa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel