Kotu ta garkame wani mutumi bayan ya zakke ma wani yaro ta hanyar luwadi

Kotu ta garkame wani mutumi bayan ya zakke ma wani yaro ta hanyar luwadi

Rundunar Yansandan jahar Kano ta tasa keyar da wani Magidanci mai suna Abdullahi Mohammed dan shekara Arba’in da biyar, 45, bayan kotu ya bada umarnin a garkame matashi a gidan yari biyo bayan kararsa da aka shigar a gabanta.

A ranar Litinin, 7 ga watan Janairu ne Yansanda suka gurfanar da Magidancin gaban kuliya manta sabo akan tuhumarsa da suke yi da zargin aikata laifin luwadi da wani matashi dan shekara Ashirin da biyar, 25, da ba’a bayyana sunansa ba.

KU KARANTA: 2019: An halaka dan jagaliyan siyasa saboda lika fastocin yan takara a Fatakwal

Legit.com ta ruwaito da wannan ne Yansanda suke tuhumar Abdullahi da laifin biya ma kansa bukata ta hanyar da bata dace ba, dukkaninsu mutane biyu da abin ya shafa mazauna garin Rogo ne, cikin karamar hukumar Rogo ta jahar Kano.

Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Pogu Lale ya bayyana ma kotu cewa wani mutumi mai suna Mustafa Shehu ne ya kai musu kara yayin da suke aiki a Caji ofis a ranar 27 ga watan Nuwambar 2018, inda yace ya kama Abdullahi yana luwadi da dansa a filin idi na garin Rogo.

“Cikakken binciken da muka gudanar ya bayyana cewar wanda ake zargi ya dade yana saduwa da yaron wanda ya kawo kara, kuma yana saduwa da yaron ne a wurare daban daban.” Inji Dansanda Pogu.

A cewar Dansandan, wannan laifi ya da ake tuhumar Abdullahi da tafkawa ya saba ma sashi na 284 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kano, don haka ya bukaci kotu ta yanke masa hukuncin daya dace, amma fa Abdullahi ya musanta wannan tuhuma, inda yace karya ake masa.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin kotun, mai sharia Muhammad Jibril ya bada umarnin a garkame masa wanda ake kara a gidan yari har zuwa ranar 30 ga watan Janairu, ranar da za’a cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel