Sojojin Najeriya sun tafka ma yan Boko Haram mummunar barna, sun kashe yan ta’adda 100

Sojojin Najeriya sun tafka ma yan Boko Haram mummunar barna, sun kashe yan ta’adda 100

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun tafka ma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram gagarumar barna a yankin jihohin Borno da Yobe a cikin wasu karanbatta da suka kwasa a yan kwanakin da suka gabata, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

Babban shelkwatar tsaro ta kasa ce ta sanar da haka a ranar Litinin, 7 ga watan Janairu, inda tace dakarun Sojin dake gudanar da aikin tsaro na musamman mai taken Operation Lafiya Dole sun kaddamar da wani muhimmin aiki na kakkabe ragowar yan ta’adda dake yankin Arewa maso gabas.

KU KARANTA: 2019: An halaka dan jagaliyan siyasa saboda lika fastocin yan takara a Fatakwal

Sojojin Najeriya sun tafka ma yan Boko Haram mummunar barna, sun kashe yan ta’adda 100

Makaman
Source: Facebook

A wannan aiki da Sojoji suka kaddamar, sun samu nasarar halaka fiye da mayakan Boko Haram guda dari, tare da lalata sansanoninsu da ababen hawansu, sa’annan sun kwato muggan makamai iri iri, daban daban daga hannunsu.

Daga cikin garuruwan da aka yi dauki ba dadi tsakanin dakarun Soji da yan ta’adda akwai Goniri cikin jahar Yobe, Damasak, Kross Kauwa da Monguno dake cikin jahar Borno, kuma dakarun da suka sha karanbattan sun fito ne daga sabuwar bataliya ta 120 data kunshi kwararrun Sojoji.

Sojojin Najeriya sun tafka ma yan Boko Haram mummunar barna, sun kashe yan ta’adda 100

Boko Haram
Source: Facebook

Sanawar ta bayyana cewa suma dakarun rundunar Sojan sama ba’a barsu a baya wajen hada ma mayakan Boko Haram jini da majina ba, inda suke taimaka ma Sojojin kasa ta hanyar zazzaga ma Boko Haram ruwan wuta daga jiragen yaki.

Bugu da kari, dakarun Sojan sama sun hana mayakan Boko Haram katabus, sun gagara motsawa koda nan da can, saboda jiragen yaki na sane da duk wani motsinsu, ta haka ne suka lalata musu motocinsu tare da yi musu ruwan wuta a duk lunguna da sakon da suka shiga.

Haka zalika kasancewar babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai nab akin, hakan ya kara ma Sojoji kaimi, zuwa yanzu yakin ya koma gefen tafkin Chadi, inda mayakan Boko Haram suka koma da buya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel