Wata mata da ta suma tun 2005 ta haihu cikin bacci, ko ta yaya hakan ta faru

Wata mata da ta suma tun 2005 ta haihu cikin bacci, ko ta yaya hakan ta faru

- Abin al ajabi baya karewa, matar da take kwance fiye da shekaru 14 bata san inda kanta yake ba ta haihu

- Matar na kwance ne a cibiyar kiwon lafiya ta Haceinda dake Arizona

- Cibiyar tace zata tsananta binciken yanda abin ya faru

- Ana zargin ko 'shedan' ne yayi mata ciki tana baccin suman

Wata mata da ta suma tun 2005 ta haihu cikin bacci, ko ta yaya hakan ta faru
Wata mata da ta suma tun 2005 ta haihu cikin bacci, ko ta yaya hakan ta faru
Asali: Twitter

Jami'an yan sanda a Phoniex dake US suna bincike akan wata mata data haihu bayan shafe shekaru 14 da tayi a sume inda ta haihu a Hacienda Healthcare.

Dangin wannan mata mai suna Arizona sun bayyana cewa ta haifi danta namiji lafiyayye a ranar Alhamis 29 ga watan Disemba.

Hukumar dake kula da wannan mata sunce duk ma'aikatan su babu wanda yasan cewa tana dauke da juna biyu sai a lokacin da take nakuda.

Majinyaciyar ta kasance a Hacienda healthcare dake Phoniex tun lokacin data suma.

A wata maganar cibiyar kiwon lafiya ta Hacienda tace zata binciki don gano lafiyar majinyaciyar.

"A matsayin ma'aikata, cibiyar kiwon ta Hacienda zata tsayu tsayin daka wajen gano gaskiyar wannan murdadden al'amarin," Mai magana da yawun iyalin Arizona, Nancy Salmon tace.

Matar majinyaciya ce a cibiyar kiwon lafiya ta Hacienda na fiye da shekaru 14. Ba a barin ma'aikata maza shiga dakunan majinyata.

Ana zargin ko wani shedanin ne yayi mata ciki tana baccin suman, wanda da a kasashenmu ne da tuni an ma binne ta an gama, tunda bamu da ilimin fahimtar ko mutum suma yayi ko mutuwa bayan awanni cikin suma, balle shekaru.

DUBA WANNAN: Dan Adam ya sake kafa tarihi a safiyar yau, an sake sauka kan wata

.Wata mata data kasance a sume tun a shekara ta 2005 ta haihu a cikin baccin nata. Hukumar yan sandan Phoniex suna binciken yanda akayi matar data shafe shekaru 14 a sume ta haihu. Hukumar dake kula da wannan mata sunce duk ma'aikatan su babu wanda yasan cewa tana dauke da juna biyu sai a lokacin da take nakuda.

'Yan sanda a Phoenix, Arizona US suna binciken yanda matar da take kwance ba tare da tasan halin da take ciki ba fiye da shekaru 14 ta haihu a wata cibiyar kiwon lafiya dake Hacienda.

Rahoton yazo ne a ranar laraba cewa wata mata da ba a bayyana sunan ta ba da tayi fiye da shekaru 14 a kwance ta haifa lafiyayyen yaro namiji a ranar 29 ga watan Disamba.

Wani ma'aikaci wanda ya bukaci a boye sunan shi yace babu ma'aikacin da yasan matar na da ciki.

"Babu ma'aikacin da yasan matar na da ciki har sai lokacin da tazo haihuwa," tace a wani shirin gidan talabijin da aka boye fuskar ta da muryar ta.

"Daga abinda aka fada min, tana ta gurnani kuma basu san abinda ke damunta ba."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel