Za'a sanya wa titi a Amurka sunan Obama, sai dai a titin ne katafaren shugaba Trump yake

Za'a sanya wa titi a Amurka sunan Obama, sai dai a titin ne katafaren shugaba Trump yake

- Amurkawa sun raina shugaba Trump

- Ya zame musu allaqaqai

- Ana wata ga wata

Za'a sanya wa titi a Amurka sunan Obama, sai dai a titin ne katafaren shugaba Trump yake
Za'a sanya wa titi a Amurka sunan Obama, sai dai a titin ne katafaren shugaba Trump yake
Asali: Depositphotos

Shugaba Trump bai gama ganin abin bakin ciki ba, bayan da aka hana shi dala biliyan 50 ta gina katangar Yajuju da yake so yayi a dazukan Amurka, wadda yace ita zata hana bakin haure shigowa kasar ba bisa ka'ida ba.

Lamari da yasa aka kasa iyar da kudurin kasafin kudin 2019, wanda kuwa ya sanya gwamnati rufe ma'aikatunta na har sai baba ta gani, saboda a doka, babu aikin da za'a yi ko kudin da za'a kashe sai in an sahale wa kudin daga majalisa.

Shi dai Trump, yaki sanya wa dukkan kasafin kudin da majalisar ta iyar, muddin babu kudin katangar tasa, wadda a baya ya taba cewa Mexico ce zata biya, lokacin yana kamfe. Amurka na ta zabga asarar kudi a kowacce rana kan wannan kiki-kaka.

DUBA WANNAN: Kasashe biyar a fadin duniya da suka fi shan wahalar ta'addanci a 2018

Kwtsam, sai kuma wai gashi za'a sanya wa titin gidansa suna, Barack Obama, makiyinsa a siyasance, wanda yace sullutu ne, bai iya komai ba, ya ma sha cewa Obama ba dan Amurka bane, musulmi ne daga Kenya aka shigo dashi a boye yana jariri.

A dai wannan shiri na Birnin New York, gwamnatin zata sanya wa titin da Trump tower take sunan Obama ne don kunyata shi Trump din, tunda birnin yana cike da yan jam'iyyar Democrats masu sassaucin ra'ayi, kuma 'yam najalisu da magajin garin duk abokan Obama da Hillary Clinton ne.

Wannan na nufin duk sanda Trump zai kwatanta wani sashe na Trump Tower, katafaren Otal dinsa, ko anan neman wannan adireshi a Internet, sai an ga sunan Obama a jiki. Hakan an tabbatar ba zai yiwa Trump dadi ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel