Kalli mutumin da Gwamna Tambuwal ya nada sabon Alkalin Alkalan jahar Sakkwato

Kalli mutumin da Gwamna Tambuwal ya nada sabon Alkalin Alkalan jahar Sakkwato

Gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya amince da nadin Mai Sharia Alkali Saidu Sifawa a matsayin sabon mukaddashin babban alkalin jahar Sakkwato, watau Alkalin Alkalan jahar Sakkwato.

Legit.com ta ruwaito daraktan watsa labaru na fadar gwamnatin jahar Sakkwato, Malam Abubakar Shekara ne ya sanar da sunan Saidu Sifawa a matsayin sabon mukaddashin Alkalin Alkalan jahar, inda yace nadin ya fara ne daga ranar 31 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Zamfara ya yi ruwan miliyoyin akan wasu Sojojin Najeriya guda 10

Darakta Shekara yace gwamnan ya nada Sifawa ne biyo bayan murabus tare da ajiye aiki da tsohon Alkalin Alkalan jahar, Mai Sharia Bello Abass yayi sakamakon cika shekaru sittin da biyar a rayuwa da yayi, haka zalika Mai Sharia Bello Duduwale ya ki amincewa a nada shi.

“Gwamna Aminu Tambuwal ya amince da nadin mai sharia Saidu Sifawa a matsayin mukaddashin babban Alkalin jahar Sakkwato daga ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2018.

“Gwamna Tambuwal ya yi wannan nadi ne duba da sashi na 271 (4) na kwaskwararren kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, gwamnan na taya Mai shari Sifawa murna bias wannan mukami daya samu, tare da masa fatan alheri.” Inji shi.

A wani labarin kuma, babban alkali kuma alkalin alkalan jahar Sakkwato, Mai sharia Bello Abass yayi murabus daga aiki bayan cimma wa’adin ajiye aiki kamar yadda dokokin aikin gwamnati ta tanadar.

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da amincin Abass a matsayinsa na Alkali mai gaskiya da adalci, Tambuwal ya bayyana haka ne a yayin bikin da aka shirya ma Alkalin na barin aiki.

Gwamnan ya nada Abass mukamin Alkalin Alkalan jahar Sakkwato ne a shekarar 2016 bayan tsohuwar Alkalin Alkalai Aisha Dahiru ta yi murabus, inda a yanzu ya ajiye aiki bayan cimma wa’adin cika shekaru sittin da biyar a rayuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel