Tsohon shugaban NNPCL ya yi maganar Naira Tiriliyan 210 da ya ‘bace’ lokacin yana ofis

Tsohon shugaban NNPCL ya yi maganar Naira Tiriliyan 210 da ya ‘bace’ lokacin yana ofis

Mele Kolo Kyari ya musanta zargin ɓacewar Naira tiriliyan 210 a NNPC, yana mai cewa matsalolin lissafi ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ya kuma musanta kashe Naira biliyan biyar wajen sauya sunan NNPC, yana cewa duk abin da aka biya sun shiga asusu

Kwamitin Majalisar Dattawa ya ce zai binciki bayanan da Kyari ya gabatar kafin yanke shawarar mataki na gaba.

Abuja - Tsohon Shugaban NNPCL Mele Kolo Kyari, a ranar Talata ya musanta zargin cewa an kasa gano yadda aka ɓatar da wasu tulin kudi da yake ofis.

Da ya je gaban Majalisar Dattawa a farkon makon nan, Mele Kolo Kyari ya ce babu wasu kuɗi da yawansu ya kai Naira tiriliyan 210 a cikin asusun NNPCL.

A cewar gidan talabijin Channels, Mele Kyari ya bayyana cewa bambance-bambancen da aka samu cikin rahotannin binciken kuɗi bai nufin sun yi kafa.

Ya ce bayanan da aka samu dangane da kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023 ba su nufin an rasa wasu kuɗi, ya ce ba komai ba ne illa matsalolin lissafi.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi ya kashe mahaifinsa shugaban APC a yanayi mai tada hankali

Da yake jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Gwamnati, Kyari ya ce babu ko sisi da ya bace daga shekarar 2019 zuwa 2025 da yake ofis.

Ya ce:

“Ina tabbatar maku cewa babu wani kuɗi da ya ɓace. Ba zai yiwu a ce irin wannan makudan kuɗi sun ɓace a lokacin da nake jagoranci ba.

Batun ya shafi shigar da lissafin kuɗi ne kawai, ba wai asarar kuɗi ba.”

Batun Naira biliyan 5 na sauya sunan NNPC

Tsohon shugaban NNPC ɗin ya kuma musanta zargin cewa an kashe Naira biliyan 5 wajen sauya sunan tsohon kamfanin NNPC zuwa NNPCL shekarar 2021.

Punch ta ce ya kuma yi bayani kan wasu tambayoyin da masu binciken kuɗi suka yi dangane da rajistar NNPCL.

A cewarsa, wasu kuɗin har kusan Naira biliyan 2.99 da aka tura ne suka jawo surutu, kuma an biya su ne ga hukumomin gwamnati da su ke da alhakin aikin.

Malam Kyari ya ce kamfanin NNPC ya fara biyan kuɗin ne a madadin Gwamnatin tarayya, daga bisani sai aka cire su daga asusun kuɗin shigar gwamnati.

Kara karanta wannan

"Adadin mutanen da suka sayi hannun jari a matatar Dangote ba su kai yadda aka so ba"

Ya ƙara da cewa zargin kashe Naira biliyan biyar wajen sauya sunan kamfanin ba gaskiya ba ne.

Kyari ya kare irin rawar da ya taka wajen tafiyar da kamfanin, inda ya ce ya gaji NNPCL a lokacin yana fama da asara, amma sai ga shi ya ci riba a lokacinsa.

Ya shaida wa kwamitin, wanda Sanata Ibrahim Dankwambo ke jagoranta, cewa kamfanin ya yi asarar kusan dala biliyan 803 a shekarar 2018 kafin zuwan sa.

A cewarsa, matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen sake fasalin ayyukan kamfanin sun taimaka wajen samar da riba mai ɗorewa a karon farko cikin shekaru 44.

Sanata Dankwambo ya ce za su duba maganganun da Kyari ya yi sai su dauki matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng